✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na halarci sulhunta Obasanjo da Atiku – Dokta Gumi

Dokta Ahmad Gumi daya ne daga cikin manyan malaman kasar nan, kuma yana daya daga cikin shugabanin addinai da aka gayyata zuwa taron sulhu a…

Dokta Ahmad Gumi daya ne daga cikin manyan malaman kasar nan, kuma yana daya daga cikin shugabanin addinai da aka gayyata zuwa taron sulhu a tsakanin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakinsa kuma dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar. Halartar sulhun ta jawo cece-ku-ce inda aka zarge shi da sauran wadanda suka halarta da karkata ga Jam’iyyar PDP wanda hakan bai dace da shugabannin addini ba. Sai dai Dokta Gumi ya musanta haka inda ya shaida wa Aminiya yadda aka yi ya halarci taron da dalilansa na halarta:

 

Ko za ka bayyana dalilin zuwanka taron sulhu da aka shirya a tsakanin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar?

Wato ka san shi Musulmi idan aka ce za a yi sulhu aka gayyace shi to ya zama wajibi ya je. Manzon Allah ya bayyana muhinmanci yin sulhu a tsakanin mutane ýto, mutum ya je, duk wanda ya yarda da Allah ya kuma je Allah zai ba shi lada mai yawa.

Har idan ma aka ji cewa shugabanni ne za su yi sulhu ai irinmu idan aka gayacce mu ya zama wajibi mu je idan har ba mu je ba mun ha’inci addini.

Ke nan yanzu kun daidaita su?

Ai su ne suke son wadanda babu ruwansu da bangaranci na siyasa domin su ’yan PDP sun san lokacin da suke kan mulki idan suka yi kuskure ina zarginsu. Su ma wadannan na yanzu idan suka yi kuskure ina zarginsu, don haka sai suka ce ni ina cikin wadanda babu ruwanmu da wani bangare na siyasa. ýSuka ce irinmu suke nema wadanda ba ’yan kanzagin PDP ba, kuma ba ’yan kanzagin APC ba. Su suke son su yi shaidar cewa da gaske ne an yi wannan sulhu.

Wace shawara ka ba su a lokacin sulhun?

A’a mun nuna musu cewa lokaci ya yi da za su yafe wa juna su kuma mance da abin da ya faru a baya domin su fuskanci gaba. Wannan shi ne abin da muka fada musu. Muka kuma shaida masu cewa daga yanzu dai mun yi shaidar sun yi sulhu kuma ba zai yi kyau ba su zo suna warwarewa daga baya. Irin haka ake so ga shugabbani amma mu a nan abin kunya ne ga irin namu shugabannin dubi abin da yake faruwa Sakkwato da Zamfara da kuma wasu jihohi. Suna ta rikici da junansu sun kuma kasa ýhada kansu amma sai ga shi wadannan sun ga wata hanya sai suka ce a zo a yi sulhu. Haka ake so ba kuma abin zargi ba ne illa ma abin koyo ne da darasi ga sauran mutane. Ita ma gwamnati duk mutanen da aka kakkama a zo a yi sulhu da su, a sake su, a yi sulhu abu ne na alheri. Kuma duk mai bata sulhu Bamaguje ne mara addini.

Obasanjo ne ko Atiku ya gayyace ka?

Dukansu biyu da suka yi niyyar yin wannan sulhu sai suka nemi a kawo malaman da babu ruwansu da bangaranci wadanda kuma aka yarda da su cewa ba suna yin abinsu b ane domin wani abu don su yi shaida, ka gane. Saboda haka sai aka bukaci su kawo wadanda suka yarda da su, shi ne aka gayyace ni da kuma Bishop Kukah da Fasto Oyedepo.

Malam amma dai ka ba su shawara dai ko shi Atikun da Obasanjon?

Eh, dukansu mun ba su shawara a kan cewa su hada kai kuma su tsaya a yi wa kasa aiki kuma muka nuna musu cewa haduwarsu ta nuna misalin cewa akwai bukatar kowa ya zo a yi sulhu a kasar nan. Sulhu ne kadai zai iya magance matsalolin kasar nan. Misali rikicin kabilanci sulhu ne zai iya magance shi. Domin kowa cewa zai yi yana ramuwa ne idan aka yi masa laifi. Amma idan aka zo aka yi sulhu sai a yafe wa juna a kuma fara sabuwar rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Ko taron na da alaka da zaben 2019?

Gare su yana da alaka da siyasa kamar yadda na samu labari, amma ni a bangarena mun je ne domin yin sulhu kuma ba na goyon bayan duk wani taro na siyasa da zai kawo rabuwar kawuna a kasar nan.

Ko Malam ya damu da kalaman batanci da suka biyo bayan halartarsa taron?

Ko a jikina, ba ni damuwa domin na san akwai mutanen da babu abin da suka iya, sai zagi da suka. Mutane na cikin matsaloli an kasa samar da hanyoyin magance matsalolin, sai dai kawai zagi. Ina sane da irin hakan kuma hakan ya sa na yi fice domin in nuna musu cewa ba hakan abin yake ba. Ba za ka iya mulkar jama’a ta hanyar zagin mutane da yi musu bi-ta-da-kulli ba. Ba ka mulkin mutane ta hanyar bi-ta-da-kulli. Kana mulki ne ta bin mutane a hankali tare da nuna musu muhinmancin yafiya da sauransu. Nakan ji dadin irin surutan da ake yi, musamman idan ana zagina domin hakan na nuna irin al’ummar da muke da ita da kuma irin halin matsi da ake ciki.

Ko kana da shawara ga ’yan Najeriya?

Ni ba zan fada wa kowa ya zabi wani ba amma kafin mutum ya zabi wani ya dubi halin da yake ciki idan ya gamsu sai ya zabi abin da ke kai idan kuma bai gamsu ba sai ya zabi canji.