✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da muka sauke Wazirin Bauchi —Masarautar  Bauchi

An tsige Wazirin Bauchin ne saboda rashin biyayya ga Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.

Masarautar  Bauchi ta bayyana cewa ta tube wazirinta, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, daga mukaminsa saboda abin da ta kira rashin da’a ga Gwamnan Bala Mohammed. 

Bayanin tsigewar na kunshe ne cikin wasikar da masarautar ta fitar mai dauke da kwanan wata 3 ga Janairu, 2023 da kuma sa hannun Sakataren masarautar, Shehu Mudi Muhammad.

Wasikar ta ce, “An umarce ni bisa wasikar Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu mai lamba: MLG/LG/S/72/T da kwanan wata 30 ga Disamba, 2022.

“Wasikar ta nuna yadda ka yi rashin da’a ga Mai Girma Gwmna da ma gwamnatin jihar, don haka aka ba da umarnin tsige ka nan take.

“Bisa la’akari da bayan da suka gabata, an cire ka daga ofis a matsayin Wazirin Bauchi da kuma Mamba a Majalisar Masarauta.”

Wata majiya mai kusanci da Alhaji Muhammadu Kirfi ta shaida wa Aminiya cewa wazirin ba ya Najeriya a lokacin da aka tube shi, amma idan Allah ya yi dawowarsa, za su zauna su tattauna kan batun.

Idan za a iya tunawa, a 2017 Sarkin Bauchi, Dokta Rilwanu Suleiman Adamu, ya dakatar da Kirfi amma daga bisani Gwamna Bala Mohammed ya dawo da shi a watan Agusta, 2022.

Kirfi ya taba rike mukamin Ministan Harkokin Waje karkashin gwamnatin Shehu Shagari da kuma Ministan Ayyuka na Musamman a gwamnatin Olusegun Obasanjo.