✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ba zan sake yin takara da Buhari ba – Nuhu Ribadu

Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara da Shugaban…

Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a 2019 ba ne, saboda yana aiwatar da abubuwan da suka kamata duka shugaba nagari ya yi.

Ribadu wanda ya yi takara da Shugaba Buhari a zaben shekarar 2011 a karkashin rusasshiyar Jam’iyyar ACN, ya ce babban alheri ne ga kasar Buhari ya sake lashe zaben 2019 da ke tafe.

Ya ce dukan wadanda ke da kishin ganin ci gaban Najeriya suna sane da irin abin da Shugaban kasa Buhari yake yi.

Da yake amsa tambayar ko zai iya jingine muradinsa na tsayawa takara saboda bai wa Shugaba Buhari damar sake dawowa mulkin kasar nan, sai ya ce, “Zan iya yin abin da ma ya fi haka.

“Hakika wannan babban dalili ne. Duk lokacin da ka gamsu da wani shugabanci, to yana da kyau ka koma gefe ka bai wa kyawawan abubuwa damar ci gaba da faruwa, kuma ni na gamsu da abubuwan da Shugaban kasa ke yi a halin yanzu.”

“Yanzu Buhari ne Shugaban kasanmu, kuma na yarda da abubuwan da yake gudanarwa dari bisa dari, don haka ba ni da wata matsala da shugabancinsa ga kasar nan,” inji Ribadu.

Haka kuma tsohon Shugaban na Hukumar EFCC ya bayyana yaki da cin hanci da rashawa a matsayin aiki mafi wuya, ya ce, “Aikin na bukatar mutum mai himma da nagarta wajen cimma nasararsa.”  

Game da kin tabbatar da Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu da majalisar dattawa ta yi, Ribadu ya ce, “Ni dai ban ga wani dalili na kin tabbatar da shi don samun damar ci gaba da gudanar da ayyukansa ba. Hakika ina tare da gwamnatin tarayya bisa bashi wannan dama na gudanar da ayyukan yaki da rashawa a karkashinsa,” a cewar Nuhu Ribadu