Hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna ketare NiDCOM ta ce babu wata hanya da za a iya kwashe ‘yan Najeriya da rikicin Sudan ya rutsa da su, tana mai cewa yunkurin yin hakan na da matukar hadari.
Wata sanarwa da shugabar NiDCOM, Abike Dabiri Erewa, ta fitar a ranar Juma’a a shafin Twitter, ta ce akwai yiwuwar duk jirgin da ya sauka a kasar a kona shi.
A cewar Dabiri, a jiya Juma’a kadai an kona duka jiragen da ke filin tashin jirage na Khartoum kuma an saka dokar hana zirga-zirga.
“Babu wani jirgin da zai iya aiki,” In ji Dabiri.
Sai dai ta kara da cewa, tuni Ofishin Jakadancin Najeriya da ke kasar ya fara daukan matakan da suka dace don tallafa wa ’yan Najeriyar.
Abike ta bayyana cewa, kungiyoyin agaji na raba abinci, ruwa da magunguna yayin da ake kokarin shawo kan bangarorin da ke fada da su ajiye makamansu.
Rahotanni sun yi nuni da cewa, ma’aikatar tsaron Pentagon ta Amurka ma na duba zabin da take da shi na kwashe dubban Amurkawa da ke kasar, sai dai Fadar White House ta ce a halin da ake ciki, babu wani shirin na kwashe ‘yan kasarta ta.
“Saboda hali na rashin tabbas da ake fusknta ta fannin tsaro a Khartoum, da kuma rufe filin tashin jirage da aka yi, kada Amurkawa da suke zaune a kasar su sa ran gwamnatin Amurka na da shirin kwashe su a halin yanzu,” a cewar Kakakin Majalisar Tsaron Amurka, John Kirby.
Sai dai ya zuwa wannan Asabar, Sojojin Sudan sun bayar da damar fara kwashe baki daga kasar.
A yau Asabar din ne dai Saudiyya ta sanar da fara aikin kwashe fararen hula na kwashe tare da maido da ‘yan kasarta gida.
Fiye da mutane 150 da suka hada da jami’an diflomasiyya da na kasashen waje ne suka isa birnin Jeddah mai tashar jiragen ruwa na kasar Saudiyya, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya suka sanar.
Sanarwar da ma’aikatar ta Saudiyya ta fitar ta ce sojojin ruwa na masarautar Saudiyya ne suka kwashe mutanen tare da samun goyon baya, inda ta sanar da isowar ‘yan kasar Saudiyya 91 da wasu ‘yan kasar waje kimanin 66, daga wasu kasashe 12.
Wadannan sun hada da Kuwait, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Tunisia, Pakistan, Indiya, Bulgaria, Bangladesh, Philippines, Canada da Burkina Faso, a hukumance.
A nata bangaren, sojojin Sudan sun sanar da cewa “Amurka, Birtaniya, Faransa da China za su kwashe jami’an diflomasiyyarsu da ’yan kasarsu da jiragensu na soji.”
Ministocin tsaron Jamus da na harkokin wajen Jamus sun ce sun gudanar da wani taro na musamman dangane da rikicin a ranar asabar da kuma tattauna yiwuwar kwashe mutanen, bayan da aka tilastawa jiragen soja uku komawa baya a ranar Laraba, inji mujallar Der Spiegel.
Kwanaki dai kasashen Amurka da Koriya ta Kudu da Japan na jibge sojoji a kasashe makwabta, kuma kungiyar Tarayyar Turai na tunanin daukar irin wannan matakin na kwashe jami’an diflomasiyya da ‘yan kasarsu daga Sudan.