✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan Najeriya na ba wa Nijar wutar lantarki

Kasashen Nijar da Benin da Togo na samun wutar lantarki daga Najeriya

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana dalilin da ya sa Najeriya take sayar wa kasashen Nijar da Benin da Togo wutar lantarki.

Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya ce ana sayar wa da kasashen wutar ne bisa yarjejeniyar cewar ba za su datse ruwan da yake shigowa Najeriya yake kuma samar wa manyan madatsun ruwata na Kainji, Jebba da kuma Shiroro karfin sarrafa wutar ba.

Garba Shehu ya ce, “Manufar yarjejeniyar da tasa muke ba su wutar ita ce cewa ba zasu gina madatsun ruwa a kan Kogin Naija ba, ita kuma Najeriya da sauran makwabtanta ba za ta yi hakan ba ga Kogin Nil da ya ratsa ta kasashen Itofiya, Sudan da Masar ba.

“Ya zuwa karshen shekara ta 2019, yawan bashin da ake bin wadannan kasashen guda uku ya kai Dala miliyan 69, ko da dai sun yi kokarin biyan kaso mai tsoka daga cikinsa.

“A yanzu haka kuma, ana bin kasashen Jamhuriyar Nijar da Benin bashin kudin wutar da ya kai Dala miliyan 16, kwatankwacin Naira biliyan daya da miliyan 200”, inji shi.

Kakakin Shugaban Kasar ya kara da cewa farashin wutar lantarkin da dukkannin kamfanoni suka samar a shekarun 2018 da 2019 a Najeriya ya haura Naira tiriliyan daya da biliyan 200.

Ya kuma ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 na Najeriya sun raba sama da kashi 90 cikin 100 na wautar da aka samar a kasar.