✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban Dapchi: Babban Kwamadan Rundunar Sojan Sama ya tare a Maiduguri

Kwamandan Rundunar Sojan Sama, Eya Mashal Sadikue Abubakar ya tare a Sansanin Sojan Sama na Maiduguri, inda nan ne cibiyar hada gangamin yunkurin neman daliban…

Kwamandan Rundunar Sojan Sama, Eya Mashal Sadikue Abubakar ya tare a Sansanin Sojan Sama na Maiduguri, inda nan ne cibiyar hada gangamin yunkurin neman daliban makarantar sakandaren mata ta garin Dapchi da aka sace a makon da ya gabata.

Kamar yadda sanarwa ta fito daga rundunar, babban kwamandan ya tare a sansanin ne da nufin samun ingantattun bayanai da za su taimaka a samu nasarar ceto matan, kamar kuma yadda hakan za ta ba shi wata damar ta karfafa wa dakarun gwiwa da shawarwari na musamman wajen gudanar da aikin ceton.

Haka shi ma Babban mai ba Shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro, Mohammed Monguno, shi ma yana tare da babban kwamandan a sansanin na Maiduguri, inda yake karfafa wa dakarun gwiwa. Haka kuma dukkan manyan jami’an na tsaro, sun dunguma zuwa garin Damaturu, inda suka kai ziyarar ban girma ga Gwamnnan Jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, inda suka tattauna dangane da al’amarin sace matan.

A wata sanarwa da Daraktan Watsa Labarai na Rundunar, Eya Bais Mashal Olatokunbo Adesanya ya turo wa Aminiya, ya bayyana cewa a Talatar da ta gabata, manyan jami’an tsaron suka rankaya zuwa garin Monguno, inda suka kaddamar da muhimman ayyuka da suka shafi tsaro a yankin, wadanda suka hada da jiragen yaki da kuma na’urorin kashe gobara da sababbin gine-ginen ofis-ofis, mazaunin dakarun sojan sama. Haka kuma ya bayyana cewa tuni an kaddamar da gagarumin aikin binciken wurare daban-daban a yankin, da nufin gano wadannan yara da aka sace a makon jiya.