✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibai sun daure malami sun lakada masa duka kan samun maki kadan

Ba za mu iya daukar wani mataki a kan wannan batu ba.

Dalibai a wata makaranta a kasar Indiya ake zargi da daure wani malamin lissafi da wani ma’aikacin makarantar a jikin bishiya sannan suka lakada musu duka saboda samun maki kadan a jarrabawarsa.

Lamarin wanda ya faru a ranar Litinin din makon jiya, daliban Makarantar Scheduled Tribe Residential School da ke garin Dumka a Jihar Jharkhand a kasar, sun yaudari malaminsu na lissafi da wani ma’aikacin makarantar zuwa harabar makarantar bisa cewa za su tattaunawa a kan makinsu a jarrabawar aji-9 da aka yi kwanan nan, sai kawai suka daure su a jikin itaciyar inda aka yi zargin sun yi musu duka.

Hotuna da bidiyo da suke zagayawa a shafukan sada zumunta sun nuna wasu mutum uku daure a wata itaciya da jar igiya da dalibai maza da dama na yawo a kusa da su dauke da sanduna masu kauri.

Bidiyon ya bazu cikin sauri, kuma duk da cewa ba a dauki hoton yadda aka yi masa dukan ba, amma binciken da ’yan sanda suka gudanar ya gano cewa da gaske daliban sun yi wa wadanda abin ya rutsa da su duka, kuma daya daga cikinsu ya bayar da sanarwa da bandeji a kansa, wanda ke nuni da cewa an buge shi da sanda.

Rikicin da daliban suka yi ya samo asali ne sakamakon wasu munanan maki da wasu daga cikinsu suka samu a jarrabawar lissafi ta aji 9.

Jaridar India Times ta ruwaito cewa dalibai 11 daga cikin ajujuwa 32 sun samu sakamakon DD, wanda ya yi daidai da gazawa, kuma ya janyo fushin daliban.

Sun dauki alhakin dukan malamin lissafi, mai suna Suman Kumar da magatakardar makarantar mai suna Soneram Chaure, wadanda suka shigar da maki a shafin Intanet na makarantar, kuma sun dauki fansa.

Suman Kumar, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na ANI cewa, “Daliban sun kira mu don yin taro kuma sun ce, sakamakonsu ya yi muni.

“Hakan ya faru ne saboda ba a sa alamar kokarinsu a cikin sakamakon ba. Shugaban makarantar ne ya yi haka. Don haka ba za mu iya daukar wani mataki a kan wannan batu ba.”

Daliban da suka fusata ba su saurari bayanan wadanda abin ya shafa ba, duk da haka, an ce sun ci gaba da daure su a jikin wata itaciya tare da dukansu da sanduna.

A binciken da ’yan sanda ke ci gaba da yi, ya nuna cewa dalibai 200 da ke makarantar Scheduled Tribe Residential School ne ke da hannu a lamarin.

Duk da cewa jami’an makarantar sun gabatar da shaidun da ’yan sanda suka tattara dangane da wannan lamari, jami’an makarantar sun yanke shawarar cewa ba za su shigar da koke a kan daliban da ke da hannu a wannan aikaaika ba, saboda hakan “zai iya lalata ayyukan daliban,” kamar yadda shugaban ofishin ’yan sanda na Gopikandar, Nityanand Bhokta, ya shaida wa manema labarai.

Da farko su kansu wadanda abin ya shafa ba su kai kara ba, amma yayin da lamarin ya yi kamari a karshe sun shigar da kara a kan dalibai 11 da suka kai musu hari.

Babu tabbas kan yaya hukuncinsu zai kasance.