✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibai sun ba gwamnati wa’adin bude manyan makarantu

Sun ce ran gwamnati zai baci idan ta ki bude manyan makarantun cikin sati biyu

Daliban Najeriya sun ba wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 14 ta  bude manyan makarantu ko ta fuskanci fushinsu a fadin kasar.

Kungiyar Daliban Kwalejojin Kimiyya da Fasaha  (NAPS) ta ce ci gaba da rufe makarantun bayan bude wuraren ibada da kasuwanni alama ce ta rashin damuwar gwamanti da harkar ilimi.

“Idan Gwamantin Tarayya ta ki sanya ranar bude manyan makarantu nan da sati biyu, to gaba daya daliban kwalejoji a fadin Najeriya za su yi zanga-zanga, kuma a shirye muke damda tsayar da kasar cik”, inji shugaban NAPS na Kasa, Olalere Adetunji.

Yayin jagorantar zanga-zangar lumanar, shugaban kungiyar ya ce, “gwamanti ta fita daga siyasar duniya ta bayyana ainihin ranar bude makarantu. Ta riga ta bayar da ka’idojin bude makarantu sakandare kuma kowa a shirye yake ya bi su”.

Daliban sun ce babu hujjar ci gaba rufe manyan makarantun, don haka Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta tashi ta yi abun da ya dace ta bude su a ci gaba da harkokin Ilimi.

“Ba za mu ci gaba da kallo ana aiwatar da munanan manufofi ba, musamman a bangaren ilimi. Ko an ki ko an so COVID-19 ta riga ta zo, kuma ita ma za a samu maganinta kamar yadda aka samu na malariya”.

Daliban sun kuma bukaci gwamnati ta dakatar da albashin malamai nan take idan suka ki komawa su ci gaba da koyarwa.