✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibai 39 ne ba a gani ba bayan harin Kaduna

Dalibai mata 23 da maza 16 ne ba a gani ba bayan da aka kwashe ragowar 180 zuwa barikin soji

Hukumomi a Jihar Kaduna ta tabbatar cewa dalibai 39 ne ba a gani ba bayan harin yan bindiga a Kwalejen Horo kan Naurorin Kula da Gandun Daji (FCFM) da ke garin Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya ce alkaluman da aka tattara bayan harin sun nuna dalibai mata 23 da maza 16 ne ba a gani ba.

Yayi karin hasken ne a kan jawabinsa na farko cewa kimanin dalibai 30 ne ba a gani ba, bayan da aka mayar da ragowar zuwa barikin soji inda  ake jinyar wasu daga cikinsu da suka samu rauni a lokacin harin.

Tun da farko Aruwan ya sanar cewa sojoji sun yi nasarar kubutar da mutum 180 da suka hada da dalibai da maaikatan kwalejin, bayan sun yi dauki ba dadi da maharan.

Aruwan ya ce gwamnatin Jihar za ta rika tuntubar hukumar gudanarwar kwalejin a-kai-a-kai, yayin da hukumomin tsaro suka tashi haikan domin kubutar da daliban da aka yi garkuwa da su.

Tun da farko da yake bayani, ya ce: Sojin Kasan Najeriya sun ceto mutum 180, galibinsu daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, Karamar Hukumar Igabi, ta Jihar Kaduna.

Ya ce: “’Yan bindigar sun far wa kwalejin ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Alhamis suka yi awon gaba da dalibai da ma’aikata.”

Shugaban FCFM, Afaka, Dokta Usman Mohammed Bello ya tabbatar wa Aminiya cewa an kwashe daliban zuwa barikin sojoji ta Rundunar Sojin Kasa ta 1.

Aruwan ya ce, “Sun kutsa kai cikin makarantar ta hanyar keta katangarsa sannan suka kutsa kai kimanin mita 600 don kai hari kan ginin farko.” 

Ya ce bayan samun kiran neman agaji, Ma’aikatarsa ta sanar da Runduna ta 1 ta Sojin Kasan da kuma Rundunar Horas da Sojin Sama ta Najeriya.

“Dakarun sun yi nasarar kubutar da mutum 180; Dalibai mata 42, dalibai maza 130 da maaikata takwas.

“Akwai kuma karin dalibai 30, maza da mata da har yanzu ba a san inda suke ba.

Aruwan ya ce wasu daga cikin daliban da aka ceto sun ji rauni kuma ana jinyar su a wani sansanin sojoji.

Ya bayyana yabon Gwamna Nasir El-Rufai ga sojojin bisa hanzarin da suka yi da kuma kubutar da mutanen su 180.

%d bloggers like this: