An samu akalla dalibai 36 da za a bai wa shaidar digiri mai daraja ta farko a yayin da jami’ar Jihar Sakkwato za ta yi bikin yaye dalibai karo na 35 da na 36 da na 37 a lokaci guda.
Farfesa Sani Dangoggo, Shugaban Jami’ar a yayin zantawarsa da manema labarai cikin birnin Shehu a ranar Talata, ya ce akwai dalibai 1,473 da za a bai wa shaidar dirigi wadanda suka kammala a cikin zangon karatu uku da suka gabata.
- Abin da Sarkin Kano ya fada wa gwamnati kan kula da matasa
- Kotu ta tsare ‘barayin kananan yara’ a gidan yari
- Za a dawo wa da Najeriya £4.2m da James Ibori ya boye a Birtaniya
A cewarsa, bikin yaye dalibai na zangon karatu har guda uku wanda za a gudanar a ranar Asabar, 13 ga watan Maris a lokaci guda, shi ne makamancinsa na farko tun bayan kafuwar jami’ar a watan Yulin shekarar 2009.
Ya sanar cewa Mataimakin Shugaba Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, yana daya daga cikin sahun manyan baki da za su gabatar da lacca a yayin bikin yaye daliban wanda zai fara gudana tun daga ranar Juma’a 12 ga watan Maris.
Kazalika, ya ce akwai wasu daidaikun mutane da za a karrama da lambar yabo ta digirin digirgir a wannan rana wacce kuma za a tabbatar da nadin Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Sanusi a matsayin Uban jami’ar.
“Bikin yaye daliban zai hada da wadanda suka kammala karatunsu a zangon karatu na 2016/2017 da 2017/2018 da kuma 2019/2020 daga tsangayoyin ilimi uku na jami’ar.”
“Daga cikin dalibai 1,473 da za a yaye, akwai 36 da suka yi fice da digiri mai daraja ta farko, kuma 529 masu digiri mai babbar daraja ta biyu da dalibai 894 masu digiri mai karamar daraja ta biyu sai kuma 14 masu digiri mai daraja ta uku,” a cewar Dangoggo.
Shugaban Jami’ar ya ce kwasa-kwasai 24 da ake karantarwa a jami’ar sun samu tabbacin Hukumar Kula da Jami’o’in Najeriya NUC wanda yana daya daga cikin ka’idodi da tsare-tsarenta.
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito, Farfesa Dangoggo ya ce ana ci gaba da kokarin bunkasa matsugunan dalibai, inda a halin yanzu ake samun dalibai 12 suna kwana a dakunan da aka tanada domin dalibai hudu kacal.