✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dala biliyan 16 ta yi layar zana a NNPC’

Gwamnatin Tarayya ta ce kamfanin man fetur na kasa NNPC, ya ki saka Dala biliyan 16 a cikin asusun tattara harajin kasar nan.Babban mai binciken…

Gwamnatin Tarayya ta ce kamfanin man fetur na kasa NNPC, ya ki saka Dala biliyan 16 a cikin asusun tattara harajin kasar nan.
Babban mai binciken kudi na kasar nan ne ya bayyana hakan a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar dokokin kasar, kamar yadda BBC ta bayyana.
Wannan tonon sililin na daga cikin abubuwan da aka bankado game da zarge-zargen almundahana da kudi da ake zargin ana tafkawa a kamfanin a cikin shekaru masu yawa .
Shi ma tsohon gwamnan babban bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi, ya yi zargin cewa kamfanin bai saka Dala biliyan 20 na kudin harajin sayar da danyen mai ba a shekarar 2014.
Hakan na daga cikin abin da ya sa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya cire shi a kan kujerarsa.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen cin hanci da karbar rashawa a kasar kuma a yanzu haka manyan jami’ai a tsohuwar gwamnatin kasar na fuskantar shari’a bisa zarge-zargen wawure dukiyar al’umma.