✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakatar da Rahama Sadau na nan – MOPPAN

kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa MOPPAN reshen Jihar Kano ta tabbatar da cewa ta dakatar da Rahama Sadau daga bayan ita Rahama ta ce…

kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa MOPPAN reshen Jihar Kano ta tabbatar da cewa ta dakatar da Rahama Sadau daga bayan ita Rahama ta ce babu wanda ya dakatar da ita ba. 

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar Alhaji Balarabe Murtala Baharu ne ya tabbatar da hakan a hirar sa da Aminiya inda ya ce shekara guda ke nan da zartar da hukuncin dakatar da ita inda aka ba ta wa’adin kwana 30 ta gurfana a gaban kwamitin da kungiyar ta kafa domin ta kare kanta amma ta ki halarta.

Kwanan baya ne dai Rahama Sadau ta yi hira da wata kafar yada labarai inda ta ce ita ba ta san da batun dakatar da ita ba.

“Ina cikin wadanda suka zauna suka tattauna kan wannan hukunci, kuma mun sanar har a Gidan Rediyo. Ta saba ka’ida da dokokin tafiyar da shirin fim a Jihar  Kano. Kusan shekara guda ke nan kuma har yanzu babu wani wanda ya ce ya mayar da ita, kuma lokacin da aka yi wannan sanarwa shugaban kungiyar mu reshen Jihar Kano Kabiru Maikaba ya fito ya fada cewa an kafa kwamiti aka ce idan Rahama tana da korafi an ba ta kwana 30 ta zo ta yi bayani gaban wannan kwamiti, amma har ya zuwa yau ba na tunanin Rahama ta zo ta gana ko tayi korafi a rubuce cewa ga abin da aka yi, kuma ga abin da take so ayi,” inji shi.

Da Aminiya ta tambaye shi ko yana ganin idan Rahama ta zo ta nemi a yafe mata, za a yafe mata? Sai ya ce “Mutum ne da dansa, sai ya ce fita ka bar min gidana, amma idan kana da dalili, ka samu wane ka yi masa bayani sai ka dawo”.

Daga karshe sai ya ce “babu wanda zai ce Rahama ba tauraruwa ba ce, babu wanda zai ce Rahama ba ta wakiltar kasa, bahaushiya ce musulma ce. Abin da ake magana shi ne idan mutum ya yi kuskure ya yarda ya yi kuskure. Allah ma ana masa laifi ya yafe ballanta dan uwanka dan Adam. Babu wani mutum da zai hana Rahama ci gaba, hasali ma tana yin abin da mutane suke yaba mata,” inji shi.