✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daidaitawar gwamnati da Kungiyar Kwadago ya yi daidai – Sheikh Jingir

A ranar Larabar da ta gabata ce Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Izala na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa daidaitawar da…

A ranar Larabar da ta gabata ce Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Izala na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa daidaitawar da aka yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago, a kan mafi karancin albashi na Naira dubu 30, ya yi daidai.

Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Jos.

Ya ce babu shakka amincewar da gwamnati ta yi da karin albashin na naira dubu 30 da kuma janye niyar fara yajin aikin da Kungiyar Kwadagon ta yi, abin yabo ne.

Sheikh Jingir ya yi bayanin cewa shi baya goyan bayan ayi yajin aiki, domin yajin aiki bala’i ne ga kasa. Kuma zai taba gwamnati da ma’aikatan da sauran al’ummar kasa baki daya.

Sai kuma ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su ji tsoran Allah su sadaukar da kan su, kan ayyukan da suke yi a ma’aikatansu, musamman ganin amincewar da gwamnatin ta yi, na karin albashin. Ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa su ji tsoran Allah, su guji kara farashin kayayyaki, sakamakon wannan karin albashi da aka yi.