✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daga sama har kasa

Wata Bahadejiya ce wani dan PDP ya ba ta Naira dari biyu, ya ce mata idan ta je wajen zabe, ta zabi PDP daga sama…

Wata Bahadejiya ce wani dan PDP ya ba ta Naira dari biyu, ya ce mata idan ta je wajen zabe, ta zabi PDP daga sama har kasa. Ko da ta je rumfar zaben, da aka ba ta takardun zabe; kawai sai ta fara dangwalawa, sai da ta cika kowane daki da ke jikin takardun daga sama har kasa. Bayan ta gama sai ta zo cikin mutane tana ba da labarin cewa: “Ni dai na yi zabe, daga sama har kasa!”
Daga Mamunu Abubakar Kafin Madaki, 08179316028