More Podcasts
Samun ingattattun malamai a makarantun firamare da sakandare na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tubalin ingantaccen kuma nagartaccen ilimi a cikin al’umma.
Ɗorewar wannan fafutuka ta samar da ingantaccen ilimi kuma ta dogara ne a kan samun haziƙan matasa da za su maye gurbin malaman da ake da su yanzu.
Sai dai a Najeriya, alamu suna nuni da yadda matasa da dama suke gudun aikin koyarwa, musamman a kananan makarantu.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Kujera Yake Neman Hana Maniyyata Sauke Farali
- DAGA LARABA: Dalilan ɓaraka a tsakanin iyayen riƙo da ’ya’yan riƙo
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari a kan dalilan da suka sa haka.
Domin sauke shirin, latsa nan