More Podcasts
Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin Najeriya kewa.
Wannan al’adar ita ce ta tashe da ake farawa da zarar watan azumi ya kai kwanaki 10.
- DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana
- DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi
Maza da mata na gudanar da wannan al’ada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da ɓatar da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo-kwararo ɗauke da ganga da kayan kaɗe-kaɗe suna bugawa suna waƙa.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan daɗaɗɗiyar al’adar, don jin inda ta samo asali, tarihinta da kuma yadda ake gudanar da ita.
Domin sauke shirin, latsa nan