More Podcasts
Domin sauke shirin latsa nan
Batun lalacewar harkar ilimi a Jihar Kebbi ya dauki hankalin ’yan Najeriya, musamman halin da daliban da ke rubuta jarrabawar sharar fagen shiga jami’a ke ciki.
An jima ana kwarmata batun lalacewar gine-gine da rashin kwararrun malamai da kayan koyarwa a makarantun gwamnatin jihar, wanda hakan ke tarnaki ga samar da ilimi mai inganci.
- NAJERIYA A YAU: Irin Shaidar Karatu Da Ake Bukatar Masu Neman Shugabanci Su Mallaka
- DAGA LARABA: Halin da karatun Boko ke ciki a Jihar Bauchi
A wannan karon, shirin Daga Laraba ya yada zango a jihar, inda ya kure wa bangaren ilimin jihar kallo domin gano abin da ya dabaibaye shi da niyyar neman mafita.