“Babban abin da yake damunmu a zaman kasa sun hada da fatara da talauci da rashin aikin yi da yunwa da rashin tsaro da tsatstsauran ra`ayi da kabilanci. Sai kuma mun yarda mun yi aiki tare, kana zamu kai ga gaci.”
Wadannan kalamai na cikin kalaman da shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yi a ranar Alhamis din makon jiya a lokacin wani taron da shugabannin kasashen duniya daga Nahiyar Afirka da Amurka da kasashen Turai da na Asiya a Abuja mai taken “Tsaron dan Adam, zaman lafiya da ci gaba-kudurin karni na 21 a Afiirka” cikin bukuwan cikar kasar nan shekaru 100, da hadewar daTurawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya a karkashin Gwamna Janar Lord Fredrick Lugard ya yi mata na hada kudanci da arewa a zaman kasa daya a ranar 14 ga Janairun 1914.
A lokacin bukuwan bayan waccan lacca an kuma bayar da lambobin yabo ga fitattun `yan kasar nan masu rai da matattu da suka bada gudummuwa ko suke kan bayar da gudummuwa akan fannoni irin nagwagwarmayar samun `yancin kai da siyasa da shugabanci da tattalin arzikin kasa da kasuwanci da sauran fannonin ci gaban kasa. Jerin sunayen da wannan fili ba zai iya kawo ma mai karatu su ba. Shi kansa shugaban kasa cewa ya yi daga jerin mutane 500, da ake ganin kowanensu ya cancanta aka daddage aka sake zabo wadancan 100, da suka hada da shugabannin mulkin mallaka na lokacin, wato, Sarauniyar Ingila Sarauniya Elizabeth da Gwaman Janar Lord Lugard da Uwargidansa Flora Shaw.
Batun shugabanni da aka karrama bisa ga irin gudummuwar da suka bayar ko suke kan bayarwa ta fannoni daban-daban na kasar nan, ba shi ne abin tsokaci ga wannan makala tawa ta yau ba, abin da na yi aniyar mayar da hankali akai, shi ne irin batutuwan da shugabannin kasashen Nahiyar Afirkan suka tattauna da matsayin da suka cimmawa da yadda za su shawo kansu a cikin karni na 21 da muke ciki, wato batun tsaron rayuka da dukiyoyin al`umma, al`amarin da ya kai fagen da yanzu kasashen duniya musamman nanahiyar Afirka suke fama da.
Tun farko a wajen bude wancan taro shugaba Jonathan ya mayar da hankalinsa ne kacokan akan irin annobar sukurkucewar matakan tsaro da kasar nan da wasu kasashe Nahiyar ta Afirka suke fuskanta, musamman batun rikicin `yan kungiyar Jam`atu Ahlis-Sunnah Lidda`awati Wal jihad da ake ma lakabi da Boko Haram, rikicin da ya ce, bayan tsoro da yake jefawa a zukatan `yan kasar nan da kawo koma bayan akan tattalin arzikin kasa yana kuma haddasa asarar daruruwan rayukan al`umma da na dukiyoyinsu, ya kuma sanya kasar nan na kashe makudan kudin da suka kai Dalar Amurka biliyan 18, duk shekara, walau ko don yakar `yan kungiyar ko bada taimako ga kasashen da suke fama da matsaloliin tsaron. Haka su ma sauran shugabannin kasashen Afirkan da suka halartar bikin, suka kuma samu tofa ta albarkacin bakunsu kokoken da sukai ta yi kenan.
Wasu daga cikin kasashen Nahiyar Afirka da yanzu suke fama da rikice-rikkice masu kama da yaki da kabilanci da addini, sun hada da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da Sudan ta Kudu da Somaliya da Gambiya, baya ga nasu kasashe irinsu Libya da Masar da Tunisiya da aka fara kusan shekaru uku da kuma har gobe cikin dar-dar kasashen suke zaune.
Don haka a wajen wancan taro da yanzu za a rika yi wa lakabi da “Matsayin da aka dauka a Abuja”shugabannin Afirkan kafatan dinsu sun amince da cewa lallai akwai manya-manyan matsalolin tsaro da suke wa Nahiyar tasu barazana, don haka suka amince da wasu daga cikin wadannan kudurori da matakan da za su aiwatar da su kamar haka:-
Shugabannin sun yarda su kafa dokar da za ta mayar da laifuffukan aikata ta`addanci a wata kasa, tamfar ta`addanci ne a dukkan kasashen Nahiyar, kuma yaki da ta`addanci, yaki ne don mulkin dimokuradiyya. Sun yanke shawarar za su sake tsarin hanyoyin daukar matakan tsaronsu, a kowace kasa ta yadda za su yaki ta`addanci. Sun jadda kudirinsu wajen ganin sun rubayya kokarinsu wajen karfafa mulkin dimokuradiyya a kasashensu, musamman wajen rage kudin tafiyar da gwamnati da gudanar da yakin neman zabe da yin zaben kansa. Sun kuma yi tsokaci akan hana bazuwar kananan makamai a hannayen jama`ar kasashensu, wanda hakan na kara rura wutar rikice-rikecen ta`addanci da nahiyar ke fuskanta.
Shugbannnin kasashen Afirkan, sun amince su kara inganta matakan tsaro akan iyakokinsu. Kazalika sun kuma amince da su kafa wata Hukuma da za ta rika bin kadin kare hakkin Bil Adama a nahiyar. Akan batun rashin ayyukan yi, shugabannin sun yi ittifakin cewa rashin ayyukan yi ga jama`arsu, suke ummal-haba`isin wajen yin barazana akan matakan tsaro, don haka sun yanke shawarar su tunkari wannan kalubale ta hanyar kara samar da guraben ayyukan yi da kuma koyar da sana`o`in hannu. Aniyar shugabannin Nahiyar Afirkan ne su kai wadannan kudurori wajen taron musamman na uku na kungiyar Tarayyar Afirkan da za a yi nan gaba kadan, ya yin da shi kuma shugaba Jonathan mai masaukin baki ake sa ran ya zuwa yanzu ya gana da shugannin kasashe Chadi da Jamhuriyar Nijar da Kamaru, kasashen da ke makwabtaka da kasar nan daga shiyyar Arewa maso yamma inda gwagwarmayar `yan Boko Haram din take ta ta`azzara a yanzu.
Mai karatu idan ka bi sannu a hankali akan jawabin shugaba Jonathan ya gabatar da sanarwar bayan taron da shi da takwarorinsa suka zartas a cikin wancan biki na cikar kasar nan shekaru 100, da hadawa, za ka san cewa shugabannimu suna sane da irin matsalolin da ke addabar talakawansu, matsalolin da ba sai na sake ambatarsu ba, illah dai kawai suna dukufa ne cikin rashin gudanar da mulki cikin kamanta gaskiya da adalci da rura wutar kabilanci da ta addini tsakankanin talakawansu, don kawai su cimma burinsu na gudanar da mulki akan radin kansu, alhali sun kwana da sanin cewa shugabannin farko ba da haka suka kafa tushen mulkinsu da a yau `yan kasashe daban-daban sukan tuna su, suna yi masu addu`o`i.
Abin da za mu fatan Allah Ya raya mu, mu gani, musamman mu nan a kasar nan (Najeriya) shi ne irin yadda Gwamanti Jonathan za ta kawo karshen yaki da gwagwarmayar `yan kungiyar Boko Haram da kuma iya tabbatar da gaskiya da adalci da hana rura wutar kabilanci da yin zabubbuka shekara mai zuwa in Allah Ya kai mu cikin gaskiya da adalci.
Daga bikin cikar Najeriya shekara100…
“Babban abin da yake damunmu a zaman kasa sun hada da fatara da talauci da rashin aikin yi da yunwa da rashin tsaro da tsatstsauran…