✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabarun magance MMM (2)

Assalamu alaikum, barka da sake haduwarmu cikin wannan fili, ga ci gaban bayani kan hanyoyin tafiyar da matsalar matasan magidanta, watau na fitar maniyyi da…

Assalamu alaikum, barka da sake haduwarmu cikin wannan fili, ga ci gaban bayani kan hanyoyin tafiyar da matsalar matasan magidanta, watau na fitar maniyyi da wuri, da fatan Allah Ya sa a dace, amin. A yau za mu duba dabarun da maigida zai yi amfani da su don ya gwanance wajen iya jan ragamar sha’awarsa. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Dabara ta 4: Tsaidau, Tsaida Matsala!
In an tuna a baya na taba yin bayani kan wannan haki mai suna tsaidau, mai matukar alfanu wajen inganta lafiyar ma’aikatar sha’awa gaba daya. Lallai binciken masana kimiyya ya tabbatar da ingancin wannan haki wajen tafiyar da matslar fitar maniyyi da wuri. Dadin dadawa, wannan bishiya akwaita ko’ina a kasar Hausa, sai kila canjin suna da ka iya samunta a garuruwa daban-daban, a wani wajen ana kiran ta da Hana Takama. Don haka sai a nemi wannan bishiya ta tsaidau, kuma a nemi ilmin yadda ake amfani da ita daga wajen masu ba da maganin gargajiya don tsayar da matsalar fitar maniyyi da wuri, da fatan Allah Ya sa a dace, amin.
Dabara ta 5: Shan kwayoyin SSRI!
A hakikanin gaskiya ba wani sanannen kwayar magani da likitoci su ka tsayar a matsayin maganin fitar maniyyi da wuri, domin shi wata matsala ce da dabi’antuwa da sabo ne su haifar da shi, shi ya sa babban magani shi ne rabuwa da wannan sabon. Amma akwai wasu jerin magunguna da aka tanada musamman don maganin tsananin huzni, damuwa da kunci, daya daga cikin side effects din shan wadannan magunguna shi ne natsantar da lazzar sha’awar ta yadda tsananin jin ta zai ragu kuma za ta runka hauhawa a hankali, wannan na tafiyar da matsalar fitar maniyyi da wuri. Ga wanda yake ganin bai iya jurewa har ya horar da kansa ya zamana ya iya jan ragama da sarrafa sha’awarsa, to yana iya zuwa ya ga likita ya yi masa bayani don ya rubuta masa ya kuma ba shi izinin shan daya daga cikin jerin wadannan magunguna da ake kira da Selectibe Serotonin Re-uptake Inhibitors. Amma fa a sani, shan wadannan magunguna ba sa taba raba mutum da wannan matsalar, dole horar da kai wajen iya jan ragamar sha’awa ne mafi tabbas din hanyar rabuwa da wannan matsala.
Dabara ta 7: Sabunta yanayin gabatarwa
Yanayin gabatarwa na al’ada, wanda aka fi sani kuma aka fi amfani da shi, ba shi da alfanu ga kawo sawwakewar wannan matsala cikin sauki da sauri, domin wani yanayi ne da ke kara takurawa da matsawa ga daukacin jijiyoyin maigida, sannan fitar da maniyyi shi ma al’amari ne da ke da nasaba da jijiyoyi, karin takura da matsi gare su nasa fitar maniyyi da wuri, don haka dole ma’auratan da ke fama da wannan matsala su bar wannan yanayi na al’ada na dan wani lokaci har sai komai ya zama daidai.
Dabara ta 8: Taimakon da uwargida za ta iya yi
Mata za ta iya taimaka wa maigidanta don ganin ya rabu da wannan matsalar ta hanyoyi da dama. Da farko dai sai ta yi masa kyakkyawar fahimta, kada ta kullace shi ko ta rika ganin kamar wani rauni ne daga bangaren mazantakarsa. Sannan ta dage da ba shi kulawa da kyautatawa ta musamman lokacin gabatawar ibadar aurensu, ta yi hakuri ta kuma dage don ganin ta taimaka masa har ya koyi yadda zai iya tarbe sha’awarsa ta yadda ba za ta rika kubce masa ba. Uwargida na iya samun lokaci don ta tausasa wa maigida dukkanin illahirin jikinsa, tausa mai kyau, don wannan zai kwantar masa da jijiyoyin jikinsa, wanda haka zai kara masa samun dama na iya tarbe sha’awarsa. Haka kuma wajen maganar horar da kai don iya jan ragamar sha’awa da bayaninsa ya zo satin da ya wuce, matar mutum na iya taimaka masa ta hanyar sarrafa wasu wurare ko gabobin da ka iya dakatar masa da sha’awarsa lokacin da ya ji ta na gab da kubce masa.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.