✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabara ta 2: Koyi da sunnar Annabi SAW (3)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin.…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin. Za mu karasa bayani kan dabara ta 2 daga inda muka kwana a makon da ya wuce:
3. Abu na uku daga Sunnar Annabi SAW da zai amfani maigida wajen zama da mata sama daya shi ne matukar hakuri: Manzon Allah SAW Ya kasance mai tsananin hakuri ga dukkanin jama’a gaba daya, musamman ga matansa RA. Annabi SAW ya kasance yana yawan hakuri da matanSa RA a cikin kowane irin hali ko yanayi, matsayinsa wajen Allah SWT da kuma cikin al’umma bai sa ya zama mai kasa yin hakuri da hali irin na ‘ya’ya mata ba, a wani hadisi, Sayyidina Umar RA ya fadi yadda ya yi wa matarsa fada a kan ta mayar masa da magana, sai ta ce da shi ai matan annabi SAW suna yi masa abin da ya fi haka ma, kuma yana yin hakuri da su. Sayyidina Umar ya cika da mamaki har sai da ya je ya tambayi ‘yarsa Ummuna Hafsat RA, ta kuma tabbatar masa da lallai hakan na faruwa. Annabi SAW ba ya yin fada ga matansa idan sun yi masa wani laifi, ba ya munana musu magana kuma ba ya hantarar su, zai musu magana cikin hakuri da sanyin rai kamar dai ba su yi masa komai ba.
A kan hakuri wajen zama da mata ne Annabi SAW ya yi wannan umarni ga magidanta: “Ku zama masu kyautata wa matanku; domin mace an halicce ta daga awaza, kuma mafi karkatuwar awaza ita ce daga samanta, don haka ku zauna da su haka nan da karkatuwarsu, domin duk wanda ya ce sai ya daidaita su to sai dai ya karya su; karyawar nan kuwa ita ce rabuwa da su.” Haka ma a hajjin bankwana da cikin wasu hadisai annabi SAW ya yi ta maimaita makamancin wannan umarni ga magidanta wajen yin hakurin zama da mata, har ma ya ce “in ka ki wani abu daga gare ta, to dole ne ka so wani abun.”
4 Bayyanawa da kayatarwa da kuma nuna soyayya salo-salo gare su: Ya kasance abu na farko da Annabi SAW yake yi idan ya shigo gidansa shi ne, zai yi aswaki ya tsabtace bakinsa, a Fahimtar wasu daga cikin malamanmu, kila yana yin hakan ne don ya sumbaci matansa ko ya kusance su cikin siga ta jin dadi, sannan ya kasance mai yawan maganganun barkwanci da matansa, yakan kuma tone su don ya sa su cikin nishadi; da yawan yin hira da su, da neman shawararsu yayin da wani abu da ya daure masa kai; yakan lura da yanayin da zuciyarsu ke ciki, da wani abu ya bata masu rai, nan da nan zai yi kokarin kawar musu da bacin ran; dubi dai yadda ya rika share wa Umma Safiyya hawaye lokacin da take kuka tana korafin ya ba ta taguwar da ba ta sauri; dubi yadda yake kiran su da sunaye na karramawa da kambamawa; dubi yadda yakan tara su a gidan duk wacce ke da aiki a ranar, a yi hira cikin annashuwa; dubi yadda yake shan ruwa da aza bakinsa daidai wajen da suka sha. Nana Aisha RA ta ba mu labarin yadda takan gwagwuyi kashi, ta bai wa Annabi SAW sai ya aza bakinsa daidai wajen da tasa nata. Yana yin ado da sanya turare musamman domin kayatar da su; yana kwanciya a jikinsu su taje masa kai da gemu ko da kuwa suna cikin jinin hailarsu ne. Duk da kasancewarsa annabi ne amma ya ba su damar da za su saki jiki da shi ta yadda ba suka daina jin shakkar tunkarar sa da kowace irin bukata tasu: dubi dai yadda suka tsare shi a kan sai ya kara masu kudin cefanen abinci, wanda a dalilin haka har ya yi fushi ya kaurace musu har tsawon wata guda. Misalai irin wannan masu dadi da ban sha’awa suna da yawa daga cikin rayuwar Fiyayyen Halitta SAW; ba su yiwuwa kawo su duka cikin wannan dan karamin filin, sai dai mu ce magidanta Hausawa a tashi a zage damtse, a yi niyya mai karfi ta koyi da wannan sunnar ta bayyanawa da kayatarwa da kuma nuna soyayya salo-salo ga matanku gaba daya; kada ku riki al’adar cewa don kun wadata matanku da komai na bukatar rayuwa wannan shi ne bayyana soyayya, wannan wani nauyi ne da Allah Ya aza muku kuka sauke kawai, amma ‘yan kananan abubuwan nan da kuke rainawa, kuke ganin bata lokaci ne, to su ne zakin zaman auren, kuma suke rayar da soyayya da sa kauna ta rika kyalli da haskaka rayuwar ma’aurata.
Ku yi koyi da masoyinmu annabi SAW, ku shagwaba matanku, kamar yadda kuka ji ya yi, ku rika jiji da su ta yadda ko da yaushe su ji suna matukar sonku da kaunarku sama da komai na rayuwar duniya, wannan ne zai sa sai su yi ta kara dagewa wajen kyautata muku, da yin abubuwan da kuke so kodayaushe, zai kuma sa su ji saukin yin ladabi da biyayya gare ku.
6. Kyautata adalci tsakaninsu: Annabi SAW Ya kasance mai yin tsayin daka sosai wajen yin adalci tsakanin matansa RA, da ba kowaccensu cikakken hakkokinta. Duk da cewa a bayyane yake A’isha ita ce mowa, amma wannan bai sa ya rika yi mata abubuwan da bai yi wa saura ba, komai daidai yake musu. Ko lokacin da yake fama da ciwon ajali ya rika raba kwana daidai tsakaninsu har sai da sauran matan suka amince ya koma dakin Ummuna Aisha gaba daya. Uwar muminai A’isha ta ruwaito cewa Annabi SAW yana adalci tsakanin matansa, sannan yakan yi addu’a da cewa: “Ya Allah, na raba daidai a cikin abin da nake iyawa, Ya Allah Kada ka zarge ni a cikin abin da ba na iyawa.”