Wani dan uwan Alhaji Atiku Abubakar ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa Atiku Abubakar ba dan Najeriya ba ne dan Kamaru ne, inda ya ce masu yada wannan jita-jitar ba su san asalin Atiku ba.
Malam Na-Sani mazaunin Unguwar Jigawar Sarki da ke Karamar Hukumar Dutse ya ce shi yaya ne ga mahaifiyar Atiku Abubakar Hajiya ’Yar Malam wadda ake wa lakabi da Kande, wadda sunanta A’isha amma sunan da aka fi sanin mahaifiyarsa da shi shi ne ’Yar Malam kasancewar ta fito ne da gidan malamai.
Na Malam Sani ya ce da shi da mahaifiyar Atiku Abubakar ’ya’yan wa da kane ne, sannan ya tabbatar da cewa mahaifin Atiku Malam Abubakar mutumin Wurno ne a Jihar Sakkwato, wanda neman ilimin littatafai ya kawo shi Dutse.
Kuma ya auri mahaifiyar Atiku a lokacin yana daukar karatu a wajen Malam Ma’aruf wato kakansu mahaifin Malam Adamu Ma’aruf wanda shi ne limamin Dutse.
Ya ce bayan ya aure ta da yake malamai irin na da masu yawo ne, sai ya tafi da ita zuwa Ganye inda a can ne Allah Ya yi zamansa, ya kafa daura yana bayar da fatawa da yada ilimin addinin Musulunci kuma ba don kannen mahaifiyar Atiku sun rasu ba, wato Azumi da Malam Iliya, ba sa yin wata uku ba su kawo mana ziyara ba kuma duk shekara Atiku yana zuwa wurinmu yana kawo mana ziyara yana taimakonmu saboda Atiku mutun ne mai zumunci da son ’yan uwa.
Ya ce daga cikin iyayen Kande wadanda aka haifi mahaifiyar Kande daki daya da su akwai Malam Adamu Ma’aruf da Malam Yusuf na Malam Nuhu da Malam Ade Malamin Jigawar Sarki, Atiku ya san wadannan kakanninsa ne na wajen uwa.
Ya ci gaba da cewa akwai kuma kannen mahaifiyar Atiku da suka hada da Muhammad Na- Sani da Malam Umar Na-Malam Yusuf da Malam Jibrin dan Alkairi da Malam Inuwa Yusuf da Haruna Adamu Liman da Hamisu Adamu da Dahiru Is’hak da Muhammed Sadik Adamu.