Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, rasuwa yana da shekara 84 a duniya.
Sarkin ya rasu ne da misalin karfe 12 na ranar Lahadi a Asibitin Sojoji da ke Kaduna.
Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu ne ya tabbatar wa Aminiya rasuwar.
- Sallar Idi: Sarkin Zazzau Ya Nesanta Kansa Da Sanarwar Limamin Masarauta
- ’Yan Sanda Sun Kama Malaman Da Suka Yi Limanci A Zaria
Daya daga cikin sarakuna mafi dadewa a kan karaga, a watan Fabrairu ya yi bikin cika shekara 45 yana mulki.
An haifi Alhaji Shehu Idris ne a 1936, kuma ya rike mukamai da dama a Najeriya.
Daga cikin mukaman da ya rike akwai Shugaban Hukumar gidan Rediyo da Talabijin ta Jihar Kaduna (KSBC), da Darakta a Hukumar Gudanarwa ta kamfanin UAC.
Ya kuma yi aiki da Baitulamalin Hukumar En’e ta Zariya, da Ma’aikatar kananan Hukumomi ta Jihar Arewa a matsayin sakatare, sannan ya rike sarautar Danmadamin Zazzau Hakimin Zariya daga 1973 zuwa 1975.