Kasar Saudiyya ta dakatar da bizar shiga kasar, inda ta sanar da hana maniyatta aikin Hajji da Umrah shiga biranen Makkah da Madina, a wani matakin hana yaduwar cutar Kurona mai alaka da numfashi.
A duk shekara miliyoyin mahajjata ne ke shiga biranen Makkah da Madina don sauke farali a kasar.
Ma’aikatar harkokin waje ta Saudiyya ta kuma ce za ta hana ‘yan kasashen da aka tabbatar akwai cutar ko tana barazana ga kiwon lafiyar al’umma zuwa kasar.
A cewar mahukuntan kasar Saudiyya sun yi hakan don kaucewar barazar yaduwar cutar da ake kira (COVID-19).