✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kurona: Yadda aka killace mutum 28 a Ogun

A jihar Ogun, an killace mutum 28 da suka yi mu’amala da dan Italiyan nan da ya shigo da cutar Kurona a jihar Legas. Gwamnan…

A jihar Ogun, an killace mutum 28 da suka yi mu’amala da dan Italiyan nan da ya shigo da cutar Kurona a jihar Legas.

Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiyodun, ya shaida cewa, dan kasar Italiya ya ziyarci kamfanin siminti na Lafarge da ke jihar inda yake aikin bada shawara a matsayinsa na kwararre a kamfanin, inda a lokacin ziyararsa ya fara nuna alamun cutar zazzabin inda aka kwantar da shi a asibitin kamfanin kafin daga bisani a garzaya da shi Legas bayan da cutar tayi kamari.

Ya ce, an killace mutum 28 da suka yi mu’amala kai tsaye da dan kasar Italiyar, kana an killace daukacin kamfanin da gidan bakin da ke ciki inda aka mayar da gidan bakin wajen ajiyar wadanda aka killace

Gwamnan ya yayi kira ga al’ummar jihar Ogun da kada su tsorata domin gwamnati na aiki tukuru dan hana yaduwar cutar.