Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta soma bincike kan labarin bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo.
Wannan na faruwa ne a kasar da ke tsaka da rikicin hare-haren ta’addanci wadda ba ta jima ba da sanar da shawo kan cutar ba.
- Ina fatan Ronaldo ya ci gaba da zama a United —Casemiro
- A gaggauta hukunta wadanda suka kashe Sheikh Aisami —JIBWIS
Hukumomin Lafiyar sun ce suna bin diddigi domin gano gaskiyar lamari a game da labarin sake kunno kai da aka ce cutar ta yi a kasar.
A farkon watan jiya ne dai mahukuntan kasar suka sanar da kawo karshen cutar ta Ebola, watanni biyu bayan mutuwar wasu mutum biyar da sanadiyar cutar a Arewa maso Yammacin kasar.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce wannan shi ne karo na 14 da ake samun Ebola a Congon tun bayan bullar ta a kasar a shekara ta 1976.
Akwai dai fargabar cewa wata mata mai shekaru 46 da ta mutu a wani asibiti da ke Beni a lardin Kivu da ke Gabashin kasar a ranar Litinin, ta harbu da kwayar cutar.
Jami’an sun ce matar ta fara rashin lafiya a hankali daga nan kuma sai ta fara nuna alamomi na cutar Ebola a tare da ita.
Ana dai samun sake bullar cutar akai- akai a kasar abin da mahukunta suka ce abin damuwa ne.
A yanzu haka an tattara wadanda matar ta yi mu’amala da su don yi musu gwaji a kan cutar.
Jami’an lafiyar sun ce a yanzu haka akwai rigakafin cutar Ebola dubu guda a kasar, inda a yanzu za a aika 200 zuwa Beni don dakile yaduwarta a garin.