✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cunkoson motoci a Abuja: An rufe gidajen mai da bankuna a Kubwa

Kwamiti na musamman da Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ya nada don magance cunkoson ababen hawa akan titunan birnin da kewaye, ya rufe wasu…

Kwamiti na musamman da Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ya nada don magance cunkoson ababen hawa akan titunan birnin da kewaye, ya rufe wasu gidajen mai 2 da kuma kasuwar zamani ta Plaza da ke da bankuna 2 a cikinsa kan zargin bada mafaka ga masu kasuwancin gefen titi.

Jagoran kwamitin Kwamred Attah Ikharo, da ya samu rakiyar rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro a yau Talata ya ce, kwamitin nasa ya dau matakin ne a sakamakon yadda a ke samun cunkoson ababan hawa a mashigar NNPC Kubwa, inda harabobin gidajen man da kuma bankunan suke.

A zantawarsa da Aminiya ya ce, matakin ya biyo bayan samun izinin wata kotun majistiri ne da ke yankin Wuse Abuja, bayan shafe wata 5 suna neman masu wuraren da su hana kasuwancin bakin hanya a gaban wurarensu da ya ce, ke haddasa cunkoson ababan hawa musamman a lokutan zirga-zirgar safe da kuma yamma.

Ya kara da cewa, matakin rufe wuraren zai ci gaba har zuwa lokacin da masu su zasu bi umarnin. Yunqurin jin ta bakin masu wuraren da wakilinmu ya yi bai samu nasara ba har zuwa lokacin hada rahoton.