✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta kashe mutum 17 a Legas

Mutum 17 ne suka mutu sakamakon cutar coronavirus a kasa da awa 48 a jihar Legas. Kwamishinan Lafiya na jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ne…

Mutum 17 ne suka mutu sakamakon cutar coronavirus a kasa da awa 48 a jihar Legas.

Kwamishinan Lafiya na jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ne ya sanar da haka ta kafar Twitter.

Ya ce a ranar Talata, 2 ga watan Yuli an samu mutum 9 da suka mutu, lamarin da ya sanya yawan wadanda suka rasu a jihar Legas suka kai mutum 59.

Bayan sa’a 24 kuma ya sake sanarwa cewa an sami karuwar mutum takwas da suka mutu, lamarin da ya sa adadin wadanda aka rasa a sakamakon cutar a Legas ya kai mutum 67.

Zuwa yanzu mutum 5,277 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Legas, yayin da aka sallami mutum 858 bayan sun warke, sai  kuma mutum 4,352 da ke ci gaba da jinyar cutar a jihar.