✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Kasashe sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama

Tsoron sake yaduwar cutar COVID-19 a karo na biyu ya kasashe soke sufurin jirage

Tsoron sake yaduwar cutar coronavirus a karo na biyu ya tilasta kasashen duniya dakatar da sufurin jiragen sama tsakaninsu.

Rahoton dawowar COVID-19 ya sa kasashe da dama daukar matakan kariya daga cutar a karo na biyu, ciki har da dakatar da sufurin jiragen sama daga kasa zuwa kasa.

Kasasen da suka shelanta dakatar da sufurin jiragen sama nan take sun hada da Indiya da Poland da Norway da Finland da Denmark.

Sun kuma dakatar da zirga-zirgar jiragensu da ke zuwa kai-tsaye zuwa kasar Ingila saboda gudun shigo da cutar daga Ingilan zuwa kasashensu.

Galibin kasashen sun dakatar da zirga-zirgar jiragen saman ne daga ranar 21 zuwa ranar 31 ga watan Disambar 2020 a wani mataki na lura da yadda lamarin cutar zai kasance a tsawon lokacin.

Ita ma kasar Saudiyya ta dakatar da masu zuwa kasarta daga kasashen waje domin gudanar da Umrah da ziyara.

Ma’aiaktar Harkokin Cikin Gidan Saudiyya ta kuma dakatar da zirga-zirgar jirage zuwa ciki da kuma fita daga kasarta na tsawon mako guda.

Haka kuma ta rufe dukkan iyakokinta da ake harkokin shige da fice na kan tudu da na teku, wanda ta ce akwai yiwuwar tsawaita wa’adin zuwa mako biyu.