✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: An sallami fursunoni 18 a Kano

An sallami fursunoni 18 a gidan gyara hali na Kurmawa da ke jihar Kano a wani matakin dakile yaduwar cutar coronavirus a jihar. Hakan ya…

An sallami fursunoni 18 a gidan gyara hali na Kurmawa da ke jihar Kano a wani matakin dakile yaduwar cutar coronavirus a jihar.

Hakan ya biyo bayan kwamitin da aka kafa karkashin jagorancin Alkali Ibrahim Sani Sarki Yola, wanda ya fara gudanar da aikin da aka dora masa inda ya fara da ziyartar gidan gyaran hali na Kurmawa.

Aminiya ta rawaito cewa, an sallami kimamin fursunoni18 daga gidan.

Babban Alkalin Alkalai na Jihar Kano Malam Abdullahi Waiya, ne ya kafa kwamitin alkalan da za su duba yiyuwar sakin wasu daga cikin fursunonin musamman masu kananan laifuka don rage cunkoso a gidajen kurkukun jihar a wani matakin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Alkali Ibrahim Sani Sarki Yola, ya bayyana cewa suna gudanar da aikin ne bisa duba masu kananan laifuka musamman wanda aka yanke musu hukunci suka kasa biyan kudin tara.

“Yanzu mun fara wannan aiki a Kurmawa, nan gaba kuma za mu je gidan gyaran hali na Goron Dutse.” In ji Alkali Ibrahim.

A jawabin kakakin Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali na Jihar Kano Musbahu Lawal Kofar Nassarawa, ya yaba wa shirin na Alkalin Alkalan duba da cewa, hakan zai rage cunkoson a gidajen gyaran halin da ke jihar.