✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cough: Sabuwar wakar Kizz Daniel ta yi zarra

Kamar dai yadda wakarsa ta 'Buga' ta yi kasuwa, haka ma sabuwar wakarsa ta 'Cough' ta kama hanya.

Fitaccen mawakin Najeriya, Oluwatobiloba Daniel, da aka fi sani da Kizz Daniel, ya dawo da zafinsa bayan da sabuwar wakarsa da ya saka mai taken ‘Cough’ ta zamo kan gaba a tsakanin takwarorinta.

Kamar dai yadda wakarsa ta ‘Buga’ ta yi kasuwa, haka ma sabuwar wakarsa ta ‘Cough’ ta kama hanya.

Tuni dai kididdga ta nuna wakar ‘Cough’ ce ta daya a cikin jerin wakokin 100 na ’yan Najeriya da suka fi daukar hankali.

A Juma’ar da ta gabata ne aka ga mawakin ya wallafa bidiyon wakar a shafinsa Instagram inda aka gan su suna cashewa da wata mace.

Sabuwar wakar na damfare ne da wani sabon salon rawa ‘Odo’ wanda tuni ya karade masu sha’awar wakokinsa.