Alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC sun nuna cewa an samu karin mutum 1,544 sabbin kamuwa da cutar Coronavirus a fadin Najeriya.
Sanarwar da NCDC ta fitar a shafinta na Twitter ta bayyana cewa cikin sa’a 24 da gabata, an samu mutum 12 da cutar ta yi ajalinsu yayin da kuma aka samu mutum 411 da suka warke kuma har an sallame su daga asibiti.
- Ko Arewa24 sun nemi in dawo Kwana Casa’in ba zan dawo ba –Safara’u
- Tsohon Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda Tambari Yabo ya rasu
An samu sabbin kamuwar ne daga wasu jihohi 21 na Najeriya ciki har da babban birnin kasar da suka hadar da; Legas (739), Filato (168), Abuja (153), Oyo (91), Nasarawa (90), Ribas (80), Kaduna (35), Edo (33) da Kano (29).
Sauran su ne; Ogun (21), Delta (19), Sakkwato (16), Akwa Ibom (11), Ebonyi (11), Enugu (10), Osun (10), Neja (9), Bauchi (8), Kebbi (8), Katsina (2), da Taraba (1).
Da wannan sabbin bayanai da Hukumar ta fitar, a halin yanzu cutar Coronavirus ta harbi mutum 97,478 a fadin kasar yayin da kuma mutum 1,342 suka riga mu gidan gaskiya tun bayan bullar cutar karon farko a wata Fabrairu.
Taskar bayanai ta Hukumar NCDC ta nuna cewa an salami 78,552 bayan sun warke, inda a halin yanzu mutum 17,584 kacal suka rage masu dauke da kwayoyin cutar a fadin kasar.