✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Italiya ta killace kanta daga duniya

Gwamnatin kasar Italiya ta fadada dokar takaita tafiye-tafiye a duk fadin kasar, inda ta killace mutum miliyan 60 a kokarinta na shawo kan yaduwar cutar…

Gwamnatin kasar Italiya ta fadada dokar takaita tafiye-tafiye a duk fadin kasar, inda ta killace mutum miliyan 60 a kokarinta na shawo kan yaduwar cutar Kurona.

Shugaban Kasar, Giuseppe Conte, ya tabbatar da dokar ta bacin wacce ake sa ran za ta takaita shige-da-ficen mutanen kasar kimanin miliyan 60 a wani yunkuri na kawar da cutar daga kasar wacce take ta farko a Nahiyar Turai mafi kamuwa da Kurona. A wani jawabi, Giuseppe Conte da aka yada ta gidan talabijin a farkon mako, ya ce matakin na killace mutanen za a iya daukarsa a matsayin “Ina zaune ne a gida.”

Mista Conte ya ce “Dole mu sauya dabi’unmu saboda mu yi himmar shawo kan wannan cuta.”

Wannan mataki ya fadada dokar takaita zirga-zirga ta Arewacin kasar inda aka fara samun barkewar cutar Kurona.

Dokar ta bayyana matakin soke duk wasu tarurrukan jama’a da wasannin motsa jiki, tare da mayar da wuraren wasannin a matsayin asibitocin wucin-gadi ga masu wasannin motsa jikin da aka samu sun kamu da cutar. Mutanen da ke da dalilan aiki ko matsalar lafiya ne kadai za a iya bari su yi zirga-zirga a tsakanin yankunan kasar Italiya ko zuwa wasu kasashen waje.

Italiya dai ta kasance daya daga aikin kasashen duniya da Kurona ta fi addaba.

… Tana raguwa a China

Shugaba Di Jinping na China ya kai ziyara Wuhan cibiyar da cutar Kurona ta barke inda ta hallaka mutane da dama a kasar.

Shugaba Di Jinpin ya kai ziyarar ce domin ganin nasarorin da aka samu kan dakile yaduwar cutar. Kafofinlabaran China sun ce Shugaba Di Jinpin ya sauka a jirgin sama daga birnin Beijing fadar gwamnati ya wuce kai-tsaye zuwa asibitin da aka gina cikin ’yan kwanaki domin magance cutar ta Cobid-19.

Ziyarar Shugaban ta zo ne lokacin da mahukunta a China suka bayyana samun raguwar sababbin masu kamuwa da cutar. Sababbin masu kamuwa da cutar sun ragu sosai a China inda a wannan Talata aka bayyana mutum 19, maimakon daruruwa a kowace rana lokacin da cutar take kamari.

Rahotanni sun ce ziyarar ita ce irinta ta farko da Shugaban ya kai bayan kwararan matakan da kasar ta dauka na dakile cutar wanda ake cewa suna yin tasiri.

 

…Ta kashe mutum 20 a Amurka

Hukumomi a Amurka sun tabbatar da mutuwar mutum na 19 yayin da jami’an gwamnatin Shugaba Trump suka ce suna fadi-tashin ganin an hanzarta samar da kayayyakin gwaje-gwajen cutar ta Kurona.

Adadin wadanda cutar ta harba a sassan rabin jihohin Amurka ya haura zuwa 400.

A baya-bayan nan jihohin Pennsylbania da Indiana da Minnesota da Nebraska suka bayyana mutane na farko da suka kamu da cutar, yayin da Florida ta samu mutum biyu da suka mutu.

Jami’an gwamnatin Amurka sun yi watsi da sukar da kwararru a fannin kiwon lafiya ke yi cewa, an bata lokaci wajen samar da kayayyakin gwaje-gwajen cutar, idan aka kwatanta da matakan da kasashe irin su Koriya ta Kudu da Jamus suka dauka.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ci gaba da yin kira ga kasashe da su tashi tsaye, inda ta bayyana cutar da wani bala’i da ya shafi duniya kamar yadda shugaban hukumar Tedros Adhanom Gebereyesus, ya shelanta haka a hedkwatar hukumar da ke Geneba.

“Muna kira ga kasashe su nemo, kuma su yi gwaji, su kuma kebe wadanda suka kamu da cutar tare da ba su kula, a kuma bi diddigin wadanda suka yi cudanya da su,” inji Shugaban.

A halin yanzu adadin mutanen da suka kamu da cutar a fadin duniya ya haura dubu 100, yayin da kusan mutum 3,500 suka mutu.

 

…Wani da ake zargin na dauke da cutar ya tsere daga asibiti

Ma’aikatar Lafiya ta Zimbabwe ta tabbatar da cewa wani mutum da ake zargin na dauke da Kurona ya tsere daga asibiti kafin a yi masa gwaji.

Mutumin mai shekara 26 ya shiga Zimbabwe ne a watan Fabrairu daga Thailand kuma ya fara zazzabi da atishawa. Bayan da ya tsere an bi shi gidansa don kamo shi; amma ba a yi nasara ba amma an bukaci  ’yan sanda su nemo shi.

Kawo yanzu dai, alkaluma sun nuna cewa an samu masu dauke da cutar 100 a fadin Afirka. Kasashen da adadinsu su ne:

· Masar – 55

· Aljeriya – 20

· Afirka ta Kudu – 7

· Tunisiya – 5

· Senegal – 4

· Maroko – 2

· Kamaru – 2

· Burkina Faso – 2

· Najeriya – 2

· Togo – 1