Tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Netherlands, Clarence Seedorf, ya musulunta.
Seedorf mai shekara 45, da kansa ya sanar da cewa ya rungumi a ddinin Musulunci, ranar Juma’a ta shafinsa na Instagram.
- Harin bam a masallacin Juma’a ya hallaka sama da mutum 50 a Pakistan
- Wainar da ake toyawa a yakin Rasha da Ukraine
Ya ce, “Ina godiya da sakonnin taya murna da aka yi ta turo min bayan na zamo daya daga cikin al’ummar Musulmi.
“Ina matukar farin cikin da kasancewa daya daga cikin ’yan uwa Musulmi na fadin duniya, ina kuma godiya ta musamman ga Sophia, wadda na samu zuzzurfan fahimtar Musulunci daga gare ta.”
Ya kuma bayyana cewa, “Ban sauya sunana ba, zan ci gaba da amfani da sunan da mahaifana suka sanya min, wato Clarence Seedorf!”
Shahararren dan wasa
Seedorf ya buga wa manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya wasa inda ya ja zarensa a tsawon lokaci.
Ya buga wa kungiyoyin kwallon kafa irin su Real Madrid, Ajax, Inter Milan da AC Milan, inda ya yi matukar tashe a lokacin.
Tsohon dan wasan tsakiyan, sau hudu yana daga kofin Gasar Zakarun Turai; Ajax, a 1995, sai Real Madrid a 1998 sannan AC Milan a 2003 da kuma 2007.
Ya kuma lashe gasar La Liga a 1997 a kungiyar Real Madrid, sannan sau biyu yana lashe gasar Serie A tare da kungiyar AC Milan a 2004 da 2011.