Shugaban Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da ‘Ogan Boye,’ ya naɗa hadimai 60 domin taimaka masa wajen gudanar da ayyukan ƙaramar hukumar.
Sanarwar naɗin ta fito ne cikin wata takardar amincewa da Sakataran Ƙaramar Hukumar, Ado Muhd Hotoro, ya sanya wa hannu.
- Rikicin siyasa tsakanin Kwankwaso, Shekarau da Ganduje na hana Kano ci gaba – Garo
- Hotunan zanga-zangar tsofaffin sojoji Abuja
An bayyana cewa naɗin ya zama wani ɓangare na shirin shugaban Ƙaramar Hukumar na inganta ci gabanta.
A cikin takardar, an ce, ’Domin tallafa wa ƙoƙarin Shugaban wajen inganta ci gaban Ƙaramar Hukumar Nassarawa, muna farin cikin sanar da naɗin waɗannan mutane zuwa muƙamai daban-daban.”
Daga cikin waɗanda aka naɗa, akwai mutum 18 da za su zama masu ɗaukar rahoto na musamman domin duba harkokin sassa daban-daban, kasuwanni, da cibiyoyin kula da lafiya a Ƙaramar Hukumar.
Sauran muƙaman sun haɗa da Mataimaki na Musamman, Shugaban Tsare-Tsare, Shugabannin Harkokin Bayanai.
Sauran sun haɗa da Sakataren Ma’aikatan Ƙaramar Hukumar, da Shugabannin Daraktoci guda takwas.
Takardar ta ƙara cewa an naɗa mutanen ne bisa cancanta, gaskiya, da jajircewa.
Shugaban ya musu kyakkyawan fata na gudanar da ayyukansu yadda ya kamata domin tallafawa ci gaban ƙaramar hukumar.