✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cire ilimin jima’i daga manhajin karatu ba daidai ba ne —Kungiyoyi

Ilimin da zai taimaka wa matasan yanke hukuncin da ya kamata a bangaren lafiyar jikinsu.

Gamayyar kungiyoyin fararen hula a Najeriya, sun yi Allah wadai da umarnin Ministan Ilimi Adamu Adamu na cire ilimin jima’i daga manhajin makarantu a kasar.

Babbar Daraktar Kungiyar Ilimi Garkuwa, Misis Toyin Chukwudozie ce ta bayyana hakan a madadin sauran kungiyoyin 53, cikin wata sanarwa da suka fitar a Abuja.

Idan ba a manta ba dai Ministan ya umarci Hukumar Habaka Binciken Ilimin Makarantu ta kasa (NERDC), a taron Hukumar Kula da Ilimi ta Kasa (NCE) karo na 66, da ta cire ilimin da ya shafi jima’i baki daya daga manhajin makarantun.

Adamu ya ce dalili shi ne ba da ilimin ya rataya ne a wuyan iyaye da malaman Addini, ba makarantun boko ba, domin gudun lalata kananan yara da ke iya amfani da wayoyi da fasahar zamani.

Sai dai Kungiyoyin ba su yi na’am da wannan ikirari na Ministan ba, inda Chukwudozie ta ce duk wanda ke da masaniyar yadda tsarin limin ya ke, na sane da cewa an saita manhajin don taimaka wa matasan tsaftataccen ilimin jima’in, da zai taimake su, ba lalata su ba.

“Da alama minista bai samu bayanai da shawarwarin da suka dace ba game da tsarin , da ma alakarsa da dakile yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki, da tasirinsa ga rayuwar matasa.

”NCE din kuma ita ce ta amince da tsarin a shekarar 2002, la’akari da yawaitar yaduwar cutar kanjamau, da cututtukan da ake da alaka da saduwa a tsakanin matasa a lokacin,” in ji ta.

Ta kuma ce manhajin bai zo da wani shiri ko tsarin da ya saba wa kowanne addini ko al’ada ba a Najeriya, sai ma samar da ilimin da zai taimaka wa matasan yanke hukuncin da ya kamata a bangaren lafiyar jikinsu.