✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin kasuwa

Wani buzu ne ya shigo motar fasinja daga Nijar zuwa Najeriya, kafin su fara tafiya sai direba ya ce musu, idan aka je kan iyaka,…

Wani buzu ne ya shigo motar fasinja daga Nijar zuwa Najeriya, kafin su fara tafiya sai direba ya ce musu, idan aka je kan iyaka, idan jami’an tsaro sun tambaye su, su ce cin kasuwa za su. Da suka zo kan iyaka kuwa, sai jami’in tsaro ya tambaya, suka ce cin kasuwa za su. Da ya leka cikin mota sai ya ga Buzu da katon nadi, sai ya ce: “Buzu sarkin gaskiya, da ka yi karya gara ka mutu, ina zuwa?” sai ya ce: “Direba ya raina mana hankali, ya ce mu gaya muku wai cin kasuwa za mu, mu kuwa Najeriya muka nufa.”
Daga Azzubair M. Fagge-Kano, 08034412272