✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cibiyar gina matasa za ta yi bikin yaye dalibai a Katsina

Cibiyar gina matasa da koyar da sana’o’in hannu, Katsina bocational Centre (KbC) za ta gudanar da bikin yaye dalibai a ranar Talata mai zuwa a…

Cibiyar gina matasa da koyar da sana’o’in hannu, Katsina bocational Centre (KbC) za ta gudanar da bikin yaye dalibai a ranar Talata mai zuwa a birnin Katsina.

Bikin, wanda shi ne karo na 11 da za a gudanar tun kafa cibiyar a 2002 zai gudana ne a karkashin shugabancin Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Shehu Shema, a yayin da kuma Sardaunan Katsina, Shugaban kungiyar Tuntuba Ta Arewa (ACF), Alhaji Ibrahim Coomassie zai kasance Babban Bako mai jawabi.
A wata takardar gayyata ta musamman da aka mika wa jaridar Aminiya, Malam danjuma Katsina, wanda shi ne mu’assasin cibiyar kuma jami’in da ke gudanar da al’amuranta, ya bayyana wa wakilinmu cewa an kafa cibiyar ne tun a shekarar 2002 da nufin tallafa wa matasa, wajen koya musu sana’o’i da dubarun rayuwar yau da kullum.
“A yayin bikin yaye daliban namu na bana, za mu karrama wasu muhimman mutane guda biyu, wadanda suke taimakawa wajen bunkasa rayuwar al’umma. Wadannan mutane kuwa su ne tsohon Shugaban Kotun daukaka kara ta Najeriya, Mai Shari’a Umaru Abdullahi da kuma Shugaban Bankin Unity Bank, Ajiyan Katsina, Alhaji Lamis Shehu Dikko.” Inji Malam danjuma.
Bikin dai zai gudana ne a dakin taro na Sakatariyar Gwamnatin Jihar Katsina da misalin karfe goma na safe, inda za a gudanar da jawabai da raba wa matasan da aka koya wa sana’o’in hannu kayan aiki da jarin kama sana’ar da suka koya domin dogaro da kansu.