Makarantar Markaz Abul Kassim al-Islamiy da ke garin Kafanchan ta gudanar da taron kara wa juna sani na kwana uku ga daliban makarantun Islamiyya da na Allo da ke cikin garin Kafanchan don cusa ladubba da karantarwar Musulunci a cikin mu’amalolinsu na yau da kullum.
Taron, wanda shi ne karo na tara, an gudanar da shi ne a dakin taro na Dubu Ebent Multipurpose Hall da ke cikin garin Kafanchan wanda kuma ya samu halartar dalibai daga dukanin makarantun Islamiyya da ke garin.
A lokacin da yake gabatar da kasida kan illolin shan miyagun kwayoyi da sauran laifuffuka da suka hada da madigo da liwadi a rana ta uku, Babban Limamin Masallacin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, Sheikh (Dokta) Mansur Isa Yalwa, ya bayyana shaye-shaye a matsayin ummulhaba’isin sauran laifuffuka da suka yiwa al’umma katutu.
Sheikh Mansur Isa ya bayyana wasu daga illolin da shan kwaya da barasa suke haifarwa da suka shafi lafiyar daidaiku da kuma ruguza tarbiyyar al’umma da jawo fyade da sauran laifuffukan da suka addabi al’umma, inda yayi kira ga matasa su guji tu’ammali da miyagun kwayoyi a matsayinsu na kashin bayan al’umma don samun rayuwa mai tsabta da kuma tsira a gobe Kiyama.
A rana ta farko da ta biyu malamai daban-daban sun gabatar da mukaloli kan batutuwan da su ma shafi ‘Hada Aure da Neman Ilimi’ da ‘Illolin Karya da Riya da Hassada’ da kuma ‘Yadda mutum zai kare kansa daga Sharrorin Shaidan.’
A jawabin, Babban Bako a wajen rufe taron, Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i wanda jami’in da ke lura da kuma sa ido a Ofishin Harkokin Addinai na Jihar Kaduna, Malam Sani Baba Jama’a, ya bayyana farin cikinsa da samun matasa masu hangen nesa wajen shirya irin wadannan tarurruka, inda ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tsabtace al’ummar jihar daga munanan ayyuka ba, inda yayi kira ga al’umma da kowa ya ba da irin tasa gudunmawa musamman iyaye, wajen magance munanan ayyuka a cikin al’umma.
“Kuma muna kira ga matasa su guji dukan abubuwan da ka iya haifar da damuwa musamman lokutan zabubbuka. Kada ku bari wadansu su yi amfani da ku kan abin da bai taka kara ya karya b,” inji shi
Da yake yi wa Aminiya karin haske, ko’adinetan shirya bitar, Malam Ahmad Tijjani Danmaikosai ya ce ganin irin tasirin da wannan taron bitar ke yi da ya hada da sadar da alheri a zukatan Musulmi tare da haifar da hadin kai da kulla zumunci kasantuwar taron wanda ba na siyasa ko wani bangare na Musulmi ba, ta sanya su tunanin karin wasu kwanaki zuwa hudu ko biyar a taro na gaba wanda suke shirin hadawa da gabatar da kasidu cikin harsunan Larabci da Ingilishi da kuma karrama wadansu fitattun mutane abin koyi.Da yake gabatar da nasa jawabin, Shugaban Cibiyar Abul Kassim, Sheikh Aminu Kassim Kafanchan ya mika godiyarsa ce ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da Shugaban Hukumar Kula da Addinai ta Jihar Kaduna Injiniya Namadi Musa saboda kyakkyawan wakilci da kuma sauran wadanda suka ba da gudunmawa tun daga Fadar Mai martaba Sarkin Jama’a da malamai masu jawabi da masu yi musu ta’aliki da masu gabatarwa da makarantun da suka turo dalibansu har zuwa daidaikun mutane da suka hada da Ciroman Jama’a Alhaji Kabiru Tanko da Danmasanin Jama’a Alhaji Shehu Usman Dahiru da sauran mahalarta.
Jama’a da dama ne suka halarci rufe taron da aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata da suka hada da kungiyoyin FOMWAN da JNI da MSSN da MYOFOSKA da Jama’a Foundation.