Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya ce babu hikima gwamnati ta ci gaba da aro kudade tana kashewa da sunan tallafi tana gadar wa ’yan baya bashi.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su fara lalubo hanyoyin taimaka wa kansu wajen dogaro da kai ba tare da sun dogara da gwamnati ba.
- Wane Ne Ke Amfana Da Kayan Shaye-Shaye A Najeriya?
- Sadiya Haruna ba ’yar Kannywood ba ce —Alhassan Kwalli
Sanusi, wanda kuma shi ne Halifan Darikar Tijjaniyya na Najeriya na wadannan kalaman ne yayin wani biki da aka shirya don murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kaddamar da littafinsa da kuma tara kudi domin wata gasar bunkasa muradun karni da aka kirkira da sunansa.
Ana sa ran tara Dalar Amurka miliyan biyu a asusun domin tallafa wa yunkurin Majalisar Dinkin Duniya wajen samar da ilimi da kuma tabbatar da daidaito tsakanin jinsuna.
A cewar tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasa (CBN), “Dole Najeriya ta fahimci cewa hanyar da muka mayar da tsarin kasarmu ba mai bullewa ba ce. Ba zai yuwu mu ci ga da biyan tallafin man fetur ba.
“Ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa yadda ake tafiyar da al’amura a yanzu ba za su dore ba.
“Ba zai yuwu a ci gaba da biyan tallafi a mai da wutar lantarki ba.
“Abubuwa ne da ake bukata, amma ba masu dorewa ba, dole mu shirya sadaukarwa a kan wasu abubuwan. Amma idan muka ki yin hakan muka ci gaba da aro kudade ba kan gado, to tabbas muna jefa makomar kasar nan cikin hatsari.
“Mataki ne matukar wahala, amma ya zama wajibi mu dauka,” inji shi.
Sanusi ya kuma ce nan da karshen shekara, alkaluman tattalin arziki na GDP na Najeriya za su fi na 1980 muni, inda ya ce sam babu hikima a ware kusan kaso 90 cikin 100 na kudaden shigar kasar wajen biyan bashi.
Ya ce, “Sam ba mu ci gaba ba. A cikin shekara biyar, an rusa dukkan wani ci gaban da muka samu a shekara 35 din da suka gabata. Irin batutuwan da ya kamata mu rika tattaunawa kenan, amma ba ma yi.
“A kullum yawan jama’a karuwa yake, tattalin arzikinmu ba ya wani ci gaba na ku-zo-ku-gani, farashin kaya na kara hauhawa kuma darajar kudinmu na dada karye wa,” inji shi.
Sanusi ya kuma ce akwai babbar barazana kan yadda karuwar haihuwar mutane ke mayar da gonaki gidaje, yayin da burtalolin kiwo ke komawa gonaki, inda ya ce wannan ne ummul-aba’isun rikicin manoma da makiyaya ba wai addini ko kabilanci ba.
Shi ma da yake nasa jawabin a taron, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya ce, “A matsayinmu na masu kula da tattalin arziki, muna da babban nauyin da ya rataya a wuyanmu wajen ganin abubuwa sun tafi kamar yadda ya kamata.”