✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta yi canjaras da Bournemouth

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bakwanci kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth, inda suka tashi canjaras da ci 2-2 a filin wasa na Vitality Stadium.…

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bakwanci kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth, inda suka tashi canjaras da ci 2-2 a filin wasa na Vitality Stadium.

Mai tsaron bayan Chelsea din wato Marcos Alonso, ne ya jefa kwallon da ta bai wa Chelsea din nasara a zagayen farko a minti na 33 da fara wasan.

Bournemouth ta farke kwallonta a ragar Chelsea ta ci, minti 9 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ta hannun dan wasanta Lerma. Marcos Alonso ya zura kwallon karshe, inda ya bai wa Chelsea nasarar farke kwallon aka tashi kunnen doki

Chelsea dai ta sha kashi a hannun Bournemouth a wasan farko da suka buga a filin wasanta na Stamford Bridge.