✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Celtic ta lashe kambun gasar Scotland bayan an katse wasanni

Hukumar gudanarwar gasar kwallon kafa ta yankin Scotland ta mika kambun gasar wa Celtic bayan da aka yanke hukuncin katse gasar dalilin cutar coronvirus. Hakan…

Hukumar gudanarwar gasar kwallon kafa ta yankin Scotland ta mika kambun gasar wa Celtic bayan da aka yanke hukuncin katse gasar dalilin cutar coronvirus.

Hakan ya sa Celtic din ta lashe gasar a karo na tara ke nan a jere.

Hukuncin katse gasar dai bai yi wa kungiyar Hearts dadi ba saboda za ta fada a gurbin gajiyayyu a karo na biyu tun shekarar 2014.

A taron da masu ruwa da tsaki a hukumar suka yi ranar Litinin ne suka zartar da hukuncin mika kambun wa kungiyar Celtic wanda hakan ya sa take da jimmilar kambun guda 51.

Kungiyar ta Celtic dai ba za ta samu damar murnar cin gasar ba saboda tun 13 ga watan Maris ‘yan wasanta suka daina atisaye tare.

Jaridar Skysport ta rawaito cewa za a dauki lokaci kafin kungiyar ta yi bikin cin gasar a hukumance.