Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ya tallafa wa bangaren kananan masana’antu, kanana da matsakaitan sana’o’i da Naira tiriliyan 2.1 a karkashin Shirin Tallafa Sana’o’i (RSSF).
Daraktan Sashen Sadarwa na CBN, Mista Osita Nwanisobi, ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a taron ‘Ranar Musamman ta CBN’, a wajen bikin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa karo na 17 na Abuja.
Nwanisobi, wanda Mataimakin Darakta Samuel Okogbue ya wakilta, ya ce an raba kudaden ne ga ayyuka 426 a fadin kasar nan.
Ya ce: “A iya sanina, a karkashin sashen sana’o’i da masana’antu, bankin ya fitar da Naira biliyan 66.99 zuwa karin ayyuka 12 na masana’antu da noma.
“Kudaden da aka tara a karkashin Cibiyar Tallafawa Sana’o’i ta RSSF a halin yanzu sun kai Naira tiriliyan 2.10 da aka raba wa ayyuka 426 a fadin kasar nan.
“A bangaren kananan masana’antu, kanana da matsakaitan sana’o’i (MSME), bankin ya tallafa wa bunkasa harkokin kasuwanci da kudi Naira miliyan 39.26 a karkashin shirin manyan makarantun kasuwanci (TIES).
“Hakan ya kawo jimillar kudaden da aka kashe a karkashinsa zuwa Naira miliyan 332.43.
“A dunkule, kudaden da aka kashe a karkashin RSSF a halin yanzu sun kai Naira tiriliyan 2.10 da aka raba wa ayyuka 426 a fadin kasar nan.”
Ya ce taken bikin baje kolin na bana, ‘Kirkirar Kasuwa Fitar da Kaya Kasashen Waje ta hanyar Zamanantar da SME,’ ya yi daidai da yunkurin bankin na habaka hanyoyin samar da albarkatu a Najeriya, tare da mai da hankali musamman wajen habaka fitar da kayayyakin da ba na mai ba.
Shugaban Kungiyar ’Yan kasuwa da Masana’antu ta Abuja (ACCI), Dokta Al-Mujtaba Abubakar, ya ce CBN ya yi amfani bangaren kanana da matsakaitan masana’antu matuka.
“Tsarin da babban bankin ya yi ya dawo da ci gaban GDP da kuma haifar da sake farfado da bangaren da ba na mai a matsayin wani muhimmin bangare na GDP,” in ji shi.