Ranar Laraban makon da ya gabata ne, bayan wani taron magoya bayansa da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki narushashshiyar jam`iyyarsu ta ANPP reshen jihar Kano a gidansa dake birnin Kano, su Malam Ibrahim Shekarau, suka tari aradu da ka, suka yanke shawarar barin sabuwar jam`iyyarsu ta hadaka, wato APC, suka koma PDP. Wannan sauyin shekar ya zo a daidai lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato kuma tsohon jagoran rusasshiyar jam`iyyar DPP, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya riga Malam Ibrahim koma APC din da kwanaki hudu, don kuwa shi tsohon gwamnan ya koma ne ranar Larabar wancan makon.
Shi ma tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubkar da ya jagoranci gwamnonin nan bakwai na jam`iyyar PDP, wajen ficewarsu daga dakin taron kasa na musammamn na jam`iyyar a bara, ficewar ita ta yi sanadiyar kafa sabuwar PDP, daga karshe kuma gwamnoni biyar daga cikin wadancan bakwai, suka canja sheka daga PDP zuwa APC, shi ma Alhaji Atiku Abubakar a ranar lahadin wannan makon ya bada shelar ficewarsa daga jam`iyyar ta PDP zuwa APC, akan dai dalilan ba adalci a cikin PDP.
Kafin canjin shekar wadancan tsofaffin gwamnoni biyu, sai da suka hadu a Sakkwato inda suka tattauna akan me zai zama makomarsu a cikin sabuwar jam`iyyar ta APC, jam`iyyar da suke cikin jiga-jigan da suka taru suka haifa. Don haka alokacin da suka bada shelar ficewarsu daga APC din a ranaikun Asabar ta wancan makon da Larabar makon day a gabata, a Sakkwato da birnin Kano. An ruwaito tsohon gwmnan jihar ta Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa yana fadawa taron manema labarai cewa babu adalci a cikin sabuwar jam`iyyar ta APC, don haka yake kaura zuwa cikin PDP. Shi ma Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, hanzarin tsohuwar jam`iyyar tasu ta APC na ta yi masu rashin adalci tunda ta dauki jagorancin jam`iyyar ta ba gwamnonin da suka shigota da rana kata, ya fadawa wani taron manema labarai a Kano. Dadin dadawa tarihin siyasar tsoffin gwamnonin biyu a wannan jamhuriyar ya tabbatar da cewa `yan jam`iyyar ANPP ne.
Malam Shekarau ya kara da cewa daga irin yadda suka kai kukansu ga uwar jam`iyyar ta APC ta kasa baki daya, kukan da ya ce ko amsar an karba ba su samu ba, bare a ce ga abin da za a yi, har zuwa lokacin da suka nade komatsansu suka fice,al`amarin da ya tabbatar da cewa ba a bukatar zamansu a cikin APC din, in kuma sun zauna ba za daukesu da wani muhimmanci ba, don haka zaman nasu baya da wani amfani.
Mai karatu idan ka manta in tunatar da kai, gwamnonin jam`iyyar PDP na jihohin Kano da Neja da Ribas da Jigawa da Adamawa da Sakkwato da Kwara, su suka tadawa uwar am`iyyarsu kayar baya a bara, bisa ga abin da suka kira rashin adalci da kama karya da neman lalle sai tsohon shugaban jam`iyyar na kasa baki daya na wancan lokacin Alhji Bamanga Tukur ya sauka daga kan karagarsa. Wannan sa`in-sa ce ta kai fagen da a ranar 26 ga watan Nuwambar barar gwamnoni biyar daga cikin wadancan bakwai in banda na jihohin Jigawa da Neja suka yi bankwana da jam`iyyar ta PDP suka koma jam`iyyar APC. Jam`iiyar da ta dauki jagorancin rasassanta na wadancan jihohi ta mika su ga sabbin gwamnonin da shigo cikin ta shigo cikinta. Wannan sauyi da aka samu yanzu shi ke haddasa tashin-tashina tsakanin jam`iyyar APC da irin wadancan jagorori da ada su aka damkawa jagorancin jihohinsu.
Bayan bayyana canjin shekar Malam Ibrahim Shekarau din da wasu mukarrabansa, daga APC din zuwa PDP, abinka da siyasa, jama`a musamman na nan Jihar Kano suna ta tofa albarkacin bakunansu akan canjin shekar. Yayin da wasu ke ganin baubaucin abin da Malamin ya yi na komawa cikin jam`iyyar shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da ala tilas zai yi tallarsa, tunda dai sun hada jam`iyya daya. Wasu kuma na ganin cewa yaushe Malam Shekarau da yake cikin sahun farko na mutanen da suka kafa APC, haka kawai a ce ya kasa jajircewa ya zauna gidan gado a yi dukkan abin da za a yi da shi ta yadda zai samu nasa rabon, amma haka kawai `yar rigimar siyasa na tasowa tun bata yi nisa ba, a ce ya canja sheka. Kai wasu ma na ganin tamfar Malam Shekarau ya yi riddar siyasa.
Maso goyan bayan Malam Shekarau din ya koma jam`iyyar PDP, suna kafa hujjar yin hakan akan baya da wani zabi da ya wuce ya yi hakan, bisa ga la`akari da irin yadda tun a shekarar 2002, da yake ma`aikacin gwamnatin jihar Kano a matsayin babban Sakatare, jin kishin-kishin din Malam Shekrau na neman ya yi takarar neman mikamin gwamnan jihar a inuwar jam`iyyar ANPP, gwamna Rabi`u Musa Kwankwaso ya sa shi gaba har sai da ya sauke shi daga kan wancan mikami na Babban Sakatare ya mayar da shi aji a zaman Malamin lissafi, daga karshe ma dai hakan tasa Malam Shekaran ya ajiye aikin ya tsunduma cikin kogin siyasar, Allah kuma cikin ikonSa ya ba shi mulkin jihar inda ya share shekaru takwas yana danawa.
A zamanin mulkin, Malam Shekarau ya binciki gwamnatin Kwankwaso na shekaru 4, binciken da ya sa wasu jami`an gwamnatin suka mayarwa da gwamnatin jihar wasu kudade.
Ni, a hawa ra`ayin, ina goyon bayan canjin shekar Malam Shekarau dari bisa dari daga APC zuwa PDP, bisa ga anba gwamna Kwankwaso jagorancin APC a jihar, ba don koma ba sai don irin abubuwan da suka wakana can baya na zamansu `yan adawa da kuma tun daga lokacin da jiga-jigan jam`iyyar APC, din na kasa suka fara zawarcin gwamnoninnan bakwai (ciki kuwa harda Gwamna Kwankwaso).Jiga-jigan da lokacin da suka zo Kano ba su nemi Malam Shekarau ba, bare a je da shi zawarcin. Kodayake daga baya an turo ayari ya ba shi hakuri. Bayan wannan ta wuce, sai ga shigar gwamna Kwankwaso dawasu takwarorinsa hudu cikin jam`iyyar APC, al`amarin da jam`iyyar ta ce jagoranci ya tashi daga kan irin su Malam Shekarau ya koma kan wadancan gwamnoni biyar.
Rashin fahimtar da ake fama da ita tsakanin Malam Shekarau da Janar Muhammadu Buhari ta sake kunno kai a cikin wannan sabuwar tafiyarsu ta APC, kamar yadda magoya bayan shugabannin biyu suka rika rura wutar rikicin a baya, yanzu ma su suka dukufa, da aniyar ganin lallai sai Janar din ya rama abinda suke ganin Malam Shekarau ya yi masa a baya. Idan ka tattara irin yadda Malam Shekarau ya samu kansa a cikin wanna sabuwar tafiyar shekarar 2015, inda a cikin gida baya da jagorancin jam`iyya, a kasa uwar jam`iyya ba ta yi da shi, idan bai kaurace wa jam`iyyar APC ba me zai yi? Ai na ji masu iya magana kan ce bukatar dara kasawa, ina amfanin Malam Shekarau da wasu magoya bayansa (tunda tuni wasu daga cikin na tare da shi a ANPP, sun bada shelar suna tare da bangaren Gwamna Kwankwaso). Ina ma a jiha Malam Shekarau zai fuskanci kalubale kawai, ba daga uwar jam`iyyarsu ta kasa baki daya, kila da al`amarin ya yi masa sauki.
Canjin shekar Shekarau
Ranar Laraban makon da ya gabata ne, bayan wani taron magoya bayansa da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki narushashshiyar jam`iyyarsu ta ANPP reshen…