Camfi na daya daga cikin al’adun Hausawa wanda ya dade kuma yake da tasiri a rayuwarsu.
Yau da kullum, musamman bayan bayyanar Musulunci da kuma ilimin zamani a kasar Hausa, tasirin camfi da yarda da shi sun yi matukar raguwa a rayuwar Hausawa.
- An yi wa kifi tiyatar da ta ci N168,000 a bakinsa
- Ranar Talata za a bude layukan sadarwa a Zamfara – Gwamna Matawalle
A wannan zamanin da muke ciki, mafi yawa daga cikin Hausawa ’yan bana-bakwai, ba su san ma me ake kira da camfi ba, don haka, mun kalato wasu daga cikin irin wadannan camfe-camfe domin kafa misali da su, musamman domin raya Adabin Hausa.
Ga wasu daga cikin camfe-camfen Malam Bahaushe:
1-Idan mutum yana lashe bayan ludayi, zai yi sanko.
2-Idan mutum yana zama a kan murhu, to zai haifi da maye.
3-Idan mace mai ciki tana zuwa dibar ruwa a kogi da dare, ’yan ruwa za su musanya mata dan da za ta haifa da aljani.
4-Idan namiji yana zama a kan kujerar mata, to zai haifi ’ya’ya mata da yawa.
5-Idan mace mai ciki ta tsallaka wurin da aka yi fitsari, to sai ta yi bari.
6-Idan karamin yaro yana cin kwai, to zai yi sata.
7-Duk wanda ya sha ruwan da gyartai ya sha ya rage, to zai yi arziki sosai.
8-Cin abinci a tsugune, yana sa abincin ya ki zama a cikin mutum, wato ya zurare.
9-Bai wa yara ruwan farko na damina, yana hana su yin laulayi.
10-Idan mutum ya yi mafarki yana cin abinci, to zai ji wata muguwar yunwa a gaba.
11-Duk mai kiran Sallah (Ladani), ba zai yi arziki ba.
12-Idan hannu na kaikayi mutum zai sami kudi.
13-Idan mutum ya yi mafarki wani ya mutu, to cikinsa ne ya kumbura.
14-Idan idonka na dama na rawa, to kudi za ka samu. Idan kuma na hagu ne, to wani mugun abu zai faru.
15-Idan ka ga kazarka tana bori, alhalin kuma a da ba ta yi, to za ka yi baƙo.
16-Idan ka yi mafarkin hakorinka ya cire, ko ka yi mafarkin danyen nama, to wani naka zai mutu.
17-Idan kana zama a dokin kofa, to aljani zai shige ka.
18-Idan mace tana fadar sunan uwar mijinta, za ta sa a yi girgizar kasa.
19-Idan ka yawaita kallon allon kabari, za ka makance.
20-Idan yaro karami yana shara, to za a yi baki a gidansu.
21-Idan mace ta yi laya da mahaifar mage, ba ta ba nakuda.
22-Idan aka shafa wa yaro jinin cibiyarsa a kan dasashi, ba shi ba kashin hakori.
23-Idan aka soya busasshen kashi aka shafe jikin yaro da shi, yaron ba zai yi kyanda ba.
24-Idan ka yi mafarkin kashi ko kuma mafarkin cewa ka fada masai, to za ka samu kudi a wannan ranar.
25-Idan kana kwana daki daya da kuturu, idan gari ya waye ka riga shi fita daga dakin, to za ka zama kuturu.
26-Duk macen da ta shiga rumbu, to za ta haifi barawo.
27-Idan namiji ya taba jelar zomo, sannan ya shafi gaban wandonsa, to zai rasa mazakuntarsa.
28-Idan ka shafa kwantsar doki a idonka, za ka iya ganin aljannu, amma fa za ka mutu.
29-Duk wanda tsawa ta kashe, za a saka shi a Aljanna.
30-Idan kana tafiya kuma kana cin abinci, to tare da Shedan kuke ci.
31-Idan mutum ya yi dariya a lokacin da yake mafarki, to wani abu da zai sa shi kuka zai faru a gare shi.
32-Idan direba ya banke kyanwa ko kare ko agwagwa da wani abin hawa, to wani mummunan abu zai same shi.
33-Idan mutum ya ci kan bera, to zai zama barawo.
34-Idan mace mara aure ta duba madubi da dare, to za ta rasa mijin aure.
35-Idan mace ta yi mafarkin maciji ya cije ta, to ta sami shigar ciki ke nan.
36-Idan mutum ya yi mafarkin shanu da giwaye ko wasu muggan namun daji, to maye ne ya kama shi ko kuma yake neman kama shi.
37-Duk wanda ya fara hada ido da mai ido daya da safe, to a ranar ba zai samu ko anini ba kuma ba wanda zai ba shi ko anini.
38-Idan mutum ya kwanta barci tare da yin filo da wandonsa, to zai yi mummunan mafarki.
39-Duk wanda ya yi shara da dare, to sa’arsa ya ke sharewa.
40-Idan mace ta haihu, to a sami danbida a sakaye a shinfidar jaririn, idan ba haka ba, to ’yan ruwa za su musanya jaririn.
41-Idan aka yi barin gishiri, to a yi sauri a share shi, idan ba haka ba, matar gidan da mijin ba za su taba zaman lafiya ba.
42-Duk ranar Laraba, a kife kaya gudun kar aljanu su yi ma fitsari.
43-A daina barin kwandon wanka a waje, idan ba haka ba kuwa aljanu su dauka su yi wanka da shi.
44-Idan mai takaba ta zauna a tabarma, to kar ka zauna, domin wani abu na iya faruwa da kai.
45-Idan mutum ya bari wani mai yin shara ya share masa kafa, to zai rasa mai aurensa.
46-Cin kasa ga karamin yaro yana kara masa kwarin gwiwa, idan kuwa ba a bar shi ya ci ba tun lokacin tatata, ba zai yi kwari ba.
47-Idan mutum yana kwana daki daya dam aye zai iya zama maye shi ma, domin kurwarsa takan fita daga jikinsa duk dare, ta tafi farauta. Kuma idan ta dawo cikin rashin sa’a tana iya jikinka.
48-Duk wanda aka kira sa sau daya ko biyu in har bai amsa ba, in an kai uku, to zai haukace ko kuma wani abu ya same shi.
49-Wanda ya kwanta cikin hasken farin wata, mura za ta kama shi.
50-Wanda ke zama a dankarin kofa zai zama gurgu.