✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Cabani ya ki amincewa da tayin Naira Miliyan 424 wajen barin Neymar a bugun fanariti

  Rahotannin da ke fitowa daga Faransa sun nuna dan kwallon kulob din PSG na Faransa Edison Cabani ya ki amiuncewa da tayin da kulob…

 

Rahotannin da ke fitowa daga Faransa sun nuna dan kwallon kulob din PSG na Faransa Edison Cabani ya ki amiuncewa da tayin da kulob din ya yi masa na ba shi kyautar Yuro miliyan 1 kwatankwacin Naira miliyan 424 don ya rika barin Neymara wajen bugun fanariti a duk lokacin da aka samu damar yin haka.

Idan za a tuna a makonni biyu da suka wuce ne Cabani da Neymar suka samu sabani a wajen buga fanariti a wasan da kulob din PSG ya yi da na Lyon a gasar rukunin Faransa da aka fi sani da Ligue 1.  Kowane daga cikinsu yana ganin shi ya fi cancanta wajen bugun fanaritin.

Rahoton ya nuna ’yan kwallon biyu sai da suka kusa ba hammata iska bayan sun yi cacar baki a game da wanda ya fi cancanta ya buga fanaritin da aka samu.

Sai dai yanzu mai kulob din Nasser Al-Khelaifi ya yi wa Cabani tayin Yuro Miliyan 1 don ya rika barin Neymar wajen bugun fanariti a duk lokacin da aka samu.  Amma Cabani ya ki amincewa da wannan tayin, inda ya nuna atafau ba zai amshi wannan tukuici ba, kuma shi ya fi cancanta ya ci gaba da yin bugun fanariti.

Neymar dai yana daukar kansa a matsayin dan kwallon da ya fi tsada a PSG da ma a duniya baki daya, al’amarin da ta sa yake ganin ya fi dacewa wajen yin bugun fanariti a kulob din yayin da Cabani kuma yake ganin ya fi dadewa a kulob din, don haka shi ne mafi cancanta a matsayin wanda zai rika buga fanariti a duk lokacin da aka samu.

Kawo yanzu dai ba a tabbatar ko an shawo kan Cabani game da wannan batu ba ko a’a.