✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buni Ya Ba Da Tallafin N100m Ga ’Yan Kasuwar Damaturu Da Gobara Ta Shafa

An ba su shaguna a Sabuwar Kasuwar Zamani da ke Damaturu da kuma tallafin kudi N100m

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayar da gudunmuwar N100m ga wadanda gobara ta yi wa barna a Kasuwar Wayoyi da ke Damaturu.

A yayin ziyarar da ya kai wurin da gobarar ta tashi domin jajanta wa wadanda abin ya shafa, gwamnan ya bayyana ta a matsayin abin takaici da kuma babbar asara ga ’yan kasuwar da lamarin ya shafa da kuma jihar baki daya.

“Abin takaici ne yadda wannan bala’i ke faruwa a yanzu yayin da matasanmu ke kokarin gina sana’o’insu,” in ji shi, kamar yadda kakakinsa, Mamman Mohammed, ya sanar.

Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnati za ta ci gaba da taimaka muku wajen dawowa kan sana’o’inku, domin samar da karin ayyukan yi ga matasan mu.”

Ya kuma umurci sakataren gwamnatin jihar da ya raba shaguna ga wadanda abin ya shafa a sabuwar kasuwar zamani ta Ibrahim Gaidam da aka gina a Damaturu.

Ya kara umartar ma’aikatar gidaje ta jihar da ta tantance irin barnar da aka yi, da nufin sake gina shagunan da abin ya shafa ga masu su.

Buni ya  kuma yi kira ga jama’a da su yi taka-tsantsan tare da daukar matakan da suka dace kan abubuwan da za su iya haddasa tashin gobara a gida da wuraren kasuwancinsu.