Gwamnatin Tarayya za ta karrama Malamin addinin musulunci, Dakta Bashir Aliyu Umar da lambar girmamawa ta OON
Malami ya tabbatarwa da Aminiya labarin samun lambar yabon ne ta wayar tarho da wakilinmu a safiyar Talata a Abuja.
- An karrama Buhari da lambar yabo mafi daraja ta Nijar
- Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa
Dakta Bashir ya ce, haka labarin ya ke, domin takarda ya samu a daren Litinin 10 ga wata ta sanar cewa an ba shi lambar yabon.
“Takardar daga Ma’aikatar Kula da Ayyuka na Musamman ta fito, mai dauke da sa hannun Ministan Ma’aikatar, hakika haka labarin ya ke,” in ji shehun malamin.
A ranar Talata 11 ga watan Okotoba ne ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai ba malamin lambar yabon, shi da sauran wadanda za a karrama, a wani gagarumin biki da za a yi a Fadar Shugaban Kasa a Abuja.
Dakta Bashir shi ne Limamin Masallacin Al-Furkan da ke Kano, yana kuma gabatar da karatuttuka da wa’azi a masallatai da kuma gidajen rediyo da talbijin.
Kazalika, yana daya daga cikin ‘yan kwamitin kula harkokin banki da kuma hada-hadar kudi bisa tsarin addinin Islama.
Yana kuma daya cikin wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen samar da tsarin karbar bashi maras ruwa na gwamnati ga musulmi.