Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nemi sahalewar Majalisar Tarayya don karbo karin bashin N2.3trn daga waje.
Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan ne ya karanta wasikar Shugaban Kasar da yake neman amincewar Majalisa, a ranar Talata bayan dawowar majalisar daga hutun sallah.
- Hisbah ta kama mutum 6 da kwalaben giya 500 a Jigawa
- El-Rufai na neman Shugaban NLC ruwa a Jallo
- Taron gwamnonin PDP bata lokaci ne —APC
- Yadda yajin aiki ya tsayar da harkoki a Kaduna
Buhari, ya ce za a yi amfani da bashin da za a karbo ne wajen cike gibin kasafin kudin 2021 wanda ya kai N5.6trn.
A cewar Buhari, hakan zai taimaka wa Gwamnatin Tarayya wajen kaddamar da manyan ayyuka da a bangarorin lafiya da ilimi.
Wannan na zuwa ne wata daya bayan Majalisar Dattawa ta amince da karbo bashin dala biliyan 1.5.
Bashin wani bangare ne na bashin dala biliyan 5.5 da kuma miliyan 995 da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbo daga waje, a watan Mayun, 2020.
Buhari, ya bukaci amincewar Majalisar domin gwamnatin ta samu damar tallafa wa gwamnatocin jihohin da ke fuskantar kalubalen kasafin kudi, sannan ta habaka wasu ayyuka.