Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da aikin shimfida titin jirgin kasa daga Arewacin Najeriya zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar ranar Talata.
Layin dogon da Gwamnatin Tarayya ta ba da aikin sa ga kamfin Mota-Engil na kasar Jamus, a kan Dala biliyan biyu zai tashi ne daga Kano ya keta ta Jihohin Jigawa da Katsina ya dangana da Jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar.
- An cafke mutanen da suka kai wa Fulani hari a Ogun
- Dalilin da ya sa ake tsoron aurenmu —Mata ’Yan Boko
- Dalilin rufe masallacin Sheikh Abduljabbar —Ganduje
‘‘Ina farin cikin sanar da cewa Shugaba Buhari zai kaddamar fara aikin shimfida layin dogo daga Kano zuwa Maradi, a ranar Talata; Aikin ya kankama,’’ inji Ministan Sufuri, Rotimi a ranar Asabar.
A Jihar Katsina ce Buhari zai kaddamar da fara aikin titin jirgin da zai biya ta garuruwan Danbatta a Jihar Kano; Kazaure a Jihar Jigawa; da kuma Daura, Mashi, Katsina da Jibiya a Jihar Katsina kafin ya shiga Jamhuriyar Nijar.
A watan Janirun 2021 ne Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da aikin mai tsawon kilomita 283.8 wanda aka sanya wata 36 a matsayin wa’adin kammaluwarsa.
Bayan amincewar, Amaechi ya wakilci Gwamnatin Tarayya wurin sanya hannu a kan yarjejeniyar aikin wanda Manajan Daraktan kamfanin Mota-Engil da zai yi aikin, Antonio Gvoea ya rattaba hannu a madadin kamfanin.
Tun a lokacin wasu ’yan Najeriya sun yi ta ce-ce-ku-ce kan amfani shimfida titin jirgin kasar ga tattalin arzikin Najeriya alhali ba a riga a sada wasu sassan Najeriya ta titin jirgin kasa ba.
Amma a jawabinsa, Amaechi ya ce za a sada layin dogon da tituna ta yadda hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da abubuwan more rayuwa a kasar.
Amaechi ya kara da cewa kamfanin zai kuma gina wata jami’a a Najeriya a yayin shimfida titin jirin, sai dai bai yi karin bayani game da hakan ba.