Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na gina sabbin gidajen yari a wasu jihohi don rage cunkoso da ake fama da shi a gidajen gyaran halin.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan, a ranar Juma’a yayin kaddamar da ginin Hedikwatar Hukumar Kula da Gyaran Hali, reshen Jihar Osun.
Ministan, ya ce Gwamnatin Buhari za ta gina sabbin gidajen yarin ne a jihohin Kano, Ribas da kuma Birnin Tarayya, Abuja.
Ya bayyana cewar gidajen yarin da ake da su an gina su ne domin daukar mutum 50,000 amma saboda yawan fursunonin da ake samu, adadin yana haura mutum 60,000.
Aregbesola ya ce gina sabbin gidajen yarin zai taimaka wajen rage cunkoson da kashi 18 cikin 100.
Wannan na zuwa ne bayan yawan kiranye-kiranye da ake yi daga ciki da wajen Najeriya kan yadda ake yawan samun cunkoson fursunoni a gidajen yarin kasar.